Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2
Transcription
Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2
Nigeria Reading and Access Research Activity Primary 2 Teacher’s Guide Jagoran Malamai - Aji 2 Nigeria Reading and Access Research Activity Primary 2 Teacher’s Guide This early grade reading material is made possible by the support of the American people through the United States Agency for International Development (USAID) under the Nigeria Reading and Access Research Activity (EdData Task Order Number 26, EHC-E-00-04-00004-00) implemented by RTI International. First edition, 2014 Second edition, 2015 Rights and permissions The text and illustrations in this work are licensed under the Creative Commons Attribution 4.0 International License. To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/ by/4.0/. Under the Creative Commons Attribution license, you are free to copy, distribute, transmit, and adapt the work as long as you attribute or credit the original author or illustrator. In the case of this book, please use the following attribution language: “Originally developed under the Nigeria Reading Access and Research Activity and licensed under the Creative Commons Attribution 4.0 International License.” Jagoran Malamai - Aji 2 Abubuwan da Ke Ciki Godiya...............................................................................................................................................i Waɗanda Suka Bayar da Gudummawa..........................................................................................ii Gabatarwa...................................................................................................................................... iii Hanyar Koyarwar RARA..................................................................................................................iv Abubuwa Biyar Na Koyar da Karatu da Rubutu............................................................................v Fahimtar ƙwayoyin Sauti.......................................................................................................................................... v Tsarin Haruffan Harshe.............................................................................................................................................. v Iya Karatu........................................................................................................................................................................ v Kalmomi......................................................................................................................................................................... vi Fahimta........................................................................................................................................................................... vi Manyan Hanyoyin Koyarwa Na Tsarin Koyar da Karatu..............................................................vi Koyo A Tare.................................................................................................................................................................... vi Gwajin Yau da Kullum..............................................................................................................................................vii In Yi, Mu Yi, Ku Yi.........................................................................................................................................................vii Amfani da Sassan Jiki...............................................................................................................................................vii Harshen Baka: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti da Sanin Kalmomi......................................................................vii Fahimtar Tsarin Rubutu...........................................................................................................................................vii Rarrafen Koyon Karatu.............................................................................................................................................vii Gwaji............................................................................................................................................. viii Gwajin Jagorancin Koyarwa..........................................................................................................ix ƙa’idojin Amfani da Allo..................................................................................................................x Dabarun Iya Rubutu.......................................................................................................................xi Alamomi.........................................................................................................................................xii Zango Na 1...................................................................................................................................... 1 Manufar Malamai da Ɗalibai......................................................................................................... 2 Mako Na 1 - Darasi Na 1 da Na 2................................................................................................................................ 6 Mako Na 2 - Darasi Na 3 da Na 4..............................................................................................................................12 Mako Na 3 - Darasi Na 5 da Na 6..............................................................................................................................18 Mako Na 4 - Darasi Na 7 da Na 8..............................................................................................................................24 Mako Na 5 - Darasi Na 9 da Na10.............................................................................................................................30 Mako Na 6 - Darasi Na 11 da Na 12.........................................................................................................................36 Mako Na 7 - Darasi Na 13 da Na 14.........................................................................................................................42 Mako Na 8 - Darasi Na 15 da Na 16.........................................................................................................................48 Alamomi........................................................................................................................................ 52 Jagoran Malamai - Aji 2 Abubuwan da Ke Ciki Zango Na 2.................................................................................................................................... 53 Manufar Malamai da Ɗalibai.................................................................................................................................. 54 Mako Na 1 Mako Na 2 Mako Na 3 Mako Na 4 Mako Na 5 Mako Na 6 Mako Na 7 Mako Na 8 - Darasi Na 1 da Na 2..............................................................................................................................56 Darasi Na 3 da Na 4..............................................................................................................................62 Darasi Na 5 da Na 6..............................................................................................................................68 Darasi Na 7 da Na 8..............................................................................................................................74 Darasi Na 9 da Na10.............................................................................................................................80 Darasi Na 11 da Na 12.........................................................................................................................86 Darasi Na 13 da Na 14.........................................................................................................................92 Darasi Na 15 da Na 16.........................................................................................................................98 Alamomi...................................................................................................................................... 104 Zango Na 3.................................................................................................................................. 105 Manufar Malamai da Ɗalibai................................................................................................................................106 Mako Na 1 Mako Na 2 Mako Na 3 Mako Na 4 Mako Na 5 Mako Na 6 Mako Na 7 Mako Na 8 Mako Na 9 - Darasi Na 1 da Na 2........................................................................................................................... 108 Darasi Na 3 da Na 4........................................................................................................................... 114 Darasi Na 5 da Na 6........................................................................................................................... 120 Darasi Na 7 da Na 8........................................................................................................................... 126 Darasi Na 9 da Na10.......................................................................................................................... 132 Darasi Na 11 da Na 12...................................................................................................................... 138 Darasi Na 13 da Na 14...................................................................................................................... 144 Darasi Na 15 da Na 16...................................................................................................................... 150 Darasi Na 17 da Na 18...................................................................................................................... 156 Rataye.......................................................................................................................................... 170 Jagoran Malamai - Aji 2 Godiya Aikin Binciken Karatu da Samun Gurbi (RARA) da Cibiyar Bincike ta RTI ta gudanar, wanda Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAID) ta ɗauki nauyi, na miƙa godiyarta ga dukkan waɗanda suka tallafa wajen samar da Jagoran Malamai na Hausa don amfanin malaman Hausa na aji biyu na firamare. Wannan littafin ya ƙunshi abubuwan da ke cikin manhajar Hausa ta makarantun firamare, wadda ake amfani da ita a makarantun Jihohin Bauchi da Sokoto, kamar yadda Hukumar Bincike da Bunƙasa Ilimi (NERDC 2012), ta samar. Haka kuma, muna godiya ga Ma’aikata Ilimi da Hukumar Ba Da Ilimin Bai-Ɗaya (SUBEB) na jihohin Bauchi da Sokoto, domin ba da gudummawar ma’aikata da shawarwari, wanda ya tabbatar da aiwatar da ayyukanmu cikin sauƙi. Daga ƙarshe, muna jinjina wa ilahirin marubuta da editoci da mazayyana hotuna da ma’aikatan bayan fage, waɗanda suka sha famar aiki wajen samar da littafin a cikin harshen Hausa. Godiya ta musamman zuwa ga ƙwararru, kamar Kwamitin Ba da Shawara Kan Koyar da Karatu (RAC/RTWG) na Jihohin Bauchi da Sokoto, waɗanda suka taimaka wajen samar da wannan Jagoran Malamai. i Jagoran Malamai - Aji 2 Waɗanda Suka Bayar da Gudummawa Sunaye Wurin Aiki Ahmad Alh. Umar State Universal Basic Education Board (SUBEB), Sokoto Alison Pflepsen RTI International Akanbi John Illustration Consultant Bilyaminu Bello Inuwa Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) ɗahiru Yalwa Mohammed College of Education, Azare Dubeck, Margaret Godwin Ondoma RTI International Desktop Publishing Consultant Hadiza Salihu Koko Shehu Shagari College of Education, Sokoto Lauwali Ibrahim State Universal Basic Education Board (SUBEB) Sokoto; Bodinga LGEA Muhammadu Bello Yusuf Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) Phyllis Hildebrandt Technical Advisor (Consultant) Prof. Malami Buba Hausa Language Consultant R. Drake Warrick Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) Raphael Aiyedipe Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) Safiya Bala State Universal Basic Education Board (SUBEB) Bauchi; Bauchi LGEA Salisu Abdullahi Tsiga Hausa Language Consultant Swadchet Sankey Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) Yahaya A. Umar State Universal Basic Education Board (SUBEB), Bauchi Zahra'u Abubakar Maishanu Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA) Jagoran Malamai - Aji 2 ii Gabatarwa ƙwarewa a karatu da muhimmancinsa wajen ilimi yana ɗaya daga cikin batutuwan da ake muhawara kansu wajen ingancin ilimi. Gwamnatocin Bauchi da Sokoto sun fahimci cewa iya karatu da rubutu ga ɗalabai na iya zama ginshiƙi wajen cigaba da karatunsu. Wannan yana da muhimmanci, ba wai wajen samun takardar shaidar kammala karatunsu ba kawai, har ma da wajen gudanar da sauran harkokin zamantakewarsu. Sai dai, binciken da aka yi na baya-bayan nan ya gano cewa, yara ƙanana ba sa iya karanta komai a cikin harshensu (Hausa) balle a harshen Ingilishi. Wannan sakamako barazana ce, wadda ke nuna cewa yaran Bauchi da Sokoto ba za su cimma burin samun ilimi na bai-ɗaya ba, sai an sami tsararriyar hanyar koyar da su karatu. Lallai akwai buƙatar sa hannun shugabanni a haɗa kai don ba da gudummawa wajen inganta harkokin koyarwa. Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAID) da gwamnatocin Bauchi da Sokoto, sun ƙulla yarjejeniya, inda suka gudanar da binciken gano iya karatun ɗalibai a matakan farko (EGRA), a aji 2 da 3 na firamare. Wannan aikin bincike na koyar da iya karatu, wato RARA, an yi ta ne domin gwada sahihan hanyoyin taimakawa da kuma samar da kayan aiki, domin inganta tsarin ilimi, ta yadda zai kawo ingancin iya karatun ɗalibai cikin harshensu na Hausa. Za a tabbatar da cimma wannan buri ta hanyar horar da malamai domin a dasa tushen amfani da: a. b. c. d. e. Fahimtar ƙwayoyin sauti Tsarin haruffan harshe Iya karatu Kalmomi Fahimta A ƙarshen wannan aikin bincike, muna fatan samun haɓakar iya karatun Hausa ga ɗalibanmu, tare da bunƙasa dabarar koyar da iya karatu ga malamanmu. Haƙiƙa ya zama wajibi mu tallafa wa aiwatar da yunƙurin RARA a makarantu, don samun cikakkiyar nasara. Alhaji Bello Yusuf Danchadi Kwamishinan Ilimi Na Jihar Sokoto iii Ibrahim Mohammed Aminu Kwamishinan Ilimi Na Jihar Bauchi Jagoran Malamai - Aji 2 Hanyar Koyarwar RARA Da Farko, shi wannan tsari ya samo asali ne daga binciken manazarta, kuma yana da nasaba da wasu ingantattun tsare-tsare da kuma la’akari da darussan da aka koya wajen gudanar da ayyukan tallafi a Najeriya. Abu Na Biyu, shi ne, tsarin yana amfani da muhimman rassan koyar da karatu don taimaka wa ɗalibai su iya karatu. Su waɗannan rassan guda biyar ne: fahimtar ƙwayoyin sauti da tsarin haruffan harshe da kalmomi da iya karatu da fahimta. Dukkansu na da tasiri a wannan tsarin na koyarwa. Abu Na Uku, shi ne, wannan tsari na koyarwa ya yi amanna da cewa maganar baka ita ce jigo wajen koyon iya karatu da rubutu. Shi ya sa wannan shiri yake ba da ƙarfi kan harshen gida, wanda shi ne Hausa. Na Huɗu, tsarin da ake bi yana ƙarfafa maganar cewa, iya karatu da rubutu a wani harshe yana taimaka wa ɗalibai su iya karatu da rubutu a wani harshen na daban. Wannan bayani ya zo daidai da hanyar nan ta ɗora sabon aiki kan abin da aka koya a baya. Abin nufi a nan shi ne, tsarin yana taimaka wa ɗalibai su koyi iya karatu a cikin harshen gida, wanda suka fi iya magana da shi tun farko, kafin su koyi karatu a harshen da ba su sani ba. Na Biyar, tsarin koyarwa na RARA, yana jaddada muhimmancin yin bayani dalla-dalla, daga tushe zuwa rassa, na darussan da za a koyar. Abin da ake nufi da irin wannan bayani shi ne, koyarwa takan fara daga sauƙaƙan ayyukan horarwa kafin a kai ga masu wuya. Tsarin na koyar da ɗalibai sabon aiki a bayyane yake, ta yadda za a fara gabatar da dukkan muhimman abubuwan da ake son a koyar tun daga farko. Shi kuma yin bayani dalla-dalla hanya ce da malamai za su shiga gaba suna aiki, ɗalibai na biye suna kwaikwayonsu. Bayan haka, sai su ɗaliban su ci gaba da koyon aikin da kansu, malamai suna dudduba su. Na Shida, wannan tsari yana ba da fifiko kan amfani da littattafai iri-iri. Ɗalibai suna buƙatar samun damar amfani da littattafan koyon karatu da suka dace da shekarunsu. Sannan kuma suna da buƙatar jin karatu daga bakin waɗanda suka iya karatu, domin su ma su kwaikwaya. Na Bakwai, tsarin ya fahimci muhimmancin gwajin ɗalibai, kuma ya shigar da gwaje-gwajen a cikin ainihin darasi, domin ya faɗakar da malamai wajen koyarwa. Na Takwas, tsarin yana sane da cewa malamai suna da buƙatar tallafi da jagora wajen koyar da karatu. Saboda haka ne ma aka tsaro shirin da niyyar ba da horo da yin jagora da kuma ba da damar musayar ra’ayi dangane da koyo da koyarwa. Na Tara, wannan tsari ya yi amanna da muhimmmancin sa-idon iyaye ga karatun ɗalibai ’yan azuzuwan farko. Ana mayar da hankali kan bai wa ɗalibai ayyukan karatu da za su gwada yi a gida. Abu Na Goma, shi ne, a fahimci cewa tsarin koyar da karatu na RARA hanya ce ta koyar da azuzuwan farko na firamare. Ba a tsara wannan hanya ta maye gurbin manhaja ba. Munyin amanna, idan aka bi wannan tsari, za a ɗora ɗalibai kan tafarkin koyon da zai kai su ga nasarar zama gwanayen karatu da rubutu. Jagoran Malamai - Aji 2 iv Abubuwa Biyar Na Koyar da Karatu da Rubutu Gabatarwa Masana sun yi amanna a kan cewa akwai abubuwa biyar da ya kamata duk wani ingantaccen shirin koyar da karatu ya ƙunsa. Domin taimaka wa ɗalibai zamowa gwanaye wajen karatu da rubutu, akwai buƙatar koyar da waɗannan rassa a cikin tsari tare da fayyacewa. Fayyacewa: Ana nufin ka yi aiki a fili don ɗalibai su koya. Tsari: Ana nufin koyarwa ta kasance ta fara daga aiki mai sauƙi zuwa mai wuya, ba tare da tsallake muhimman ayyuka ba. Abubuwan biyar su ne: a.Fahimtar ƙwayoyin sauti b. Tsarin haruffan harshe c. Iya karatu d. Kalmomi e. Fahimta 1. Fahimtar ƙwayoyin Sauti Manufa: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti na nufin iya gane ɗaiɗaikun sautukan da ake amfani da su wajen gina kalmomi. Akwai buƙatar taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar ƙwayoyin sautin da akan gina kalma. Ɗaliban da ba su da wannan masaniya za su sha wahalar koyon karatu. Kafin ɗalibai su san manyan rassan sautuka, kamar gaɓar kalma da kalma da jimla, ya kamata su san ɗaiɗaikun sautukan haruffa. Dalili: Ɗalibai na buƙatar fahimtar muhimmancin ƙwayoyin sauti domin taimaka wa karatu da rubutunsu. Hanyar Koyarwa: Ana iya bunƙasa fahimtar ƙwayoyin sauti ta hanyar amsa-amo da waƙoƙi, tare da aiki da ɗaiɗaikun haruffa. Ɗaliban da ke da fahimtar ƙwayoyin sauti na iya gane kalmomin “mace” da “mama” dukkansu suna farawa da sauti iri ɗaya /m/. 2. Tsarin Haruffan Harshe Manufa: Iya karatu na buƙatar fahimtar tsarin haruffan harshe - wato haruffa wakilan sautuka ne a cikin kalma. Wannan tsari na koyarwa, hanya ce ta karantar da ɗalibai yadda za su danganta rubutacciyar kalma da sautinta. Dalili: Koyar da ilimin sauti zai bai wa ɗalibai damar furta sauti da baƙin kalmomin da ba a koyar ba. Hanyar Koyarwa: Malamai su taimaka wa ɗalibansu ta hanyar koyar da su ɗaiɗaikun haruffa da zanen haruffa, da kuma gaɓar kalma. Haka kuma, ya dace su ba su damar koyon haɗa haruffa da rarraba su. Ɗaliban da aka koyar da su iya furta sauti na iya karantawa da kiran sunan haruffan baƙuwar kalma kamar ‘gwamma’, ko da kuwa ba su san ma’anar kalmar ba. 3. Iya Karatu Manufa: Iya Karatu, shi ne iya karanta rubutu dai-dai, cikin hanzari, tare da kakkarya murya. Dalili: Yakan taimaka wa ɗalibai fahimtar ma’anar abinda ke rubuce. Haka kuma yakan taimaka musu su zamo suna sane da tsarin jimla, wanda hakan ke taimaka wa rubutunsu da fahimtarsu. v Jagoran Malamai - Aji 2 Hanyar Koyarwa: Gwargwadon yin ma’amalar ɗalibai da rubutu, gwargwadon zamansu gwanayen karatu. Gwama karatun amshi da karatu tare da karatun raɗa zai taimaka wa ɗalibai su ƙara ƙwarewa a karatu (dubi akwatin bayani a ƙasa). Gwanaye a karatu na iya karya murya da hanzarin karatu, yayi dai dai da kalmomi da kuma yanayin karatu.. Karatun Amshi: Ana amfanin da ita a lokacin da aka gabatar da sabon rubutu. Da farko, malamai za su karanta, su kuma ɗalibai su amsa. Karatun Tare: A nan kowa zai karanta rubutun a lokaci guda. Muryar malami/malama ta taimaki ɗalibai. Karatu A ƙungiyance : Za a ga ɗalibai suna karatun rubutu a ƙungiyance. Karatun Raɗa: ɗalibai ba su da isasshiyar ƙwarewar iya karatu a asirce. Sai dai suna iya yi wa rubutu ‘karatun raɗa’, wato a tsanake. 4. Kalmomi Manufa: Kalmomi kan taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar abin da suka saurara, ko suka karanta. Haka kuma, kalmomi suna taimaka musu koyon karatu da iya magana da kuma rubutu. Dalili: ɗalibai na buƙatar sanin tarin kalmomi domin fahimtar abin da suka karanta da kuma iya bayyanar da ra’ayoyinsu. Hanyar Koyarwa: Za a iya koyar da kalmomi kai tsaye ko kuma a fakaice. Darussan da ke gwama koyarwa ta hanyar motsin jiki da amfani da hotuna da karatu a bayyane, suna bai wa ɗalibai damar jin kalmomi da amfani da su. Ya kasance, ajinku cike yake da rubutu ko’ina a baje domin amfanin ɗalibai. Ɗaliban da aka koya wa karanta kalmomi za su fi gane yawancin abin da suka saurara, ko kuma suka iya karantawa. Haka kuma, ɗalibai na iya amfani da kalmomin a lokacin rubutunsu. 5. Fahimta Manufa: Fahimta ita ce iya ganowa da bayyana ma’anar labari. Fahimta iri biyu ce. Fahimtar Zahiri ita ce wadda ke nuna iya ba da bayanin abin da ke bayyane a cikin labari (kamar launin rigar wani cikin labari, ko kuma abin da ya faru a ciki). Fahimtar hasashe kuwa ita ke buƙatar mai karatu ya nemo wani bayani da ba ya cikin labari (kamar yadda yake tsammanin wanin cikin labari ke ji, ko abin da su za su yi da a ce su ne wani a cikin labarin). Dalili: Shi ne babban dalilin yin karatu. Hanyar Koyarwa: Ya kamata a koyar da fahimta ga ɗalibai, kome ƙuruciyarsu. Ana koyar da fahimta kafin karatu da lokacinsa da kuma bayan kammala shi. Ɗaliban da aka koya wa iya amfani da fahimta, zai iya hasashen makomar labari, ya kuma auna fahimtarsa game da labarin, yayin da yake cikin karatu, tare da bayyana ra’ayinsa bayan ya kammala karatun labarin. Manyan Hanyoyin Koyarwa A Tsarin Koyar da Karatu Akwai hanyoyin koyarwa da dama da ake amfani da su wajen Ayyukan Binciken Karatu Na RARA. • Koyo a tare • Gwajin yau da kullum • In Yi, Mu yi, Ku Yi • Amfani da sassan jiki • Harshen baka: Fahimtar ƙwayoyin sauti da sanin kalmomi • Rarrafen koyon karatu • Fahintar tsarin rubutu Koyo A Tare Kamar yadda sunan ya nuna, tare ake koyo da koyarwa. Koyo a tare na ba da dama ga ɗalibai su yi aiki tare da ‘yan ajinsu kullum, ko kuma na ɗan lokaci, a ajin koyar da karatu. Yana daga cikin Jagoran Malamai - Aji 2 vi tsarin ‘In Yi, Mu Yi, Ku Yi, ko dai kafin a fara wani aiki, ko kuma bayan an kammala shi. Koyo a tare yana ƙarfafa koyo, yayin da yake ƙara samar da damar koyon amfani da sababbin bayanai tare da wasu. Yana kuma taimakawa wajen rage matsalolin da ke tattare da aji mai ɗalibai da yawa. Gwajin Yau da Kullum Ayyukan gwaji na yau da kullum a kan cusa su ne a cikin darussan koyarwa na kowace rana. Darussan Jumu’a su ake keɓewa a matsayin darussan bita da na gwajin ƙwarewar ɗalibai. Mafi yawancin ayyukan ranar Juma’a na “Ku Yi” ne, inda ake sa ran ɗalibai su yi aikin da kansu, da yake sun share mako suna koyon irin waɗannan ayyuka. Wannan yakan ba da dama ga malamai su kimanta da rubuta ƙwazon ɗalibai a lokacin da suke kammala ayyukan da aka ba su. In Yi, Mu Yi, Ku Yi Hanyar koyon karatu ta daki-daki, ita ce aka fi sani da sunan “In Yi, Mu Yi, Ku Yi”. Da farko, ɗalibai za su ga malami/malama yana aikinsa shi kaɗai. Sannan, sai su yi aikin tare da malami/malama da sauran ‘yan aji. Daga ƙarshe, kowane ɗalibi/ɗaliba zai gwada yin aikin shi kaɗai. Wannan hanyar ce aka fifita a yawancin ayyukan koyo, kamar yadda aka nuna a sashen ‘Hanyar Koyarwa’ na wannan Jagoran Malamai. Hanyar tana taimakon koyon karatu, domin tana ƙara ƙarfafa gwiwar ɗalibai yayin da suke fama da sabon aiki. Amfani da Sassan Jiki Koyarwa ta hanyar amfani da sassan jiki ya ƙunshi ayyukan da ke buƙatar ɗalibai su yi amfani da hanyoyi biyu ko fiye na ji a jiki, don fahimtar sabon bayani. Ta ƙunshi yi wa ɗalibai jagora don amfani da ganinsu da jinsu da kuma gaɓɓan jiki. Ana amfani da waɗannan hanyoyi a duk tsawon darasi. An jima ana amfani da hanyar koyarwar da ta haɗa ji da gani da motsi da tafi, ga waɗanda aka haifa da ƙarancin fahimta. Yanzu an gano cewa kowane ɗalibi/ɗaliba na iya samun amfanin koyarwa ta wannan hanya. Harshen Baka: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti da Sanin Kalmomi Iya karanta kalmomi yakan zo cikin sauƙi idan an sami ingantaccen horon iya magana. Bunƙasa fahimtar ƙwayoyin sauti da kalmomi shi ke samar da tushe ga koyon karatu. Fahimtar ƙwayoyin sauti na nufin samun fahimtar dangantakar da ke akwai tsakanin sautukan harshe da rassa, kamar gaɓoɓin kalma da raujin sautuka cikin kalma. Haka kuma ɗalibai na buƙatar su sami damar koyo da amfani da kalmomi. Sanin kalmomi na taimaka wa ɗalibai lokacin da suka fara karatu. Fahimtar Tsarin Rubutu Ganin harshe a rubuce na taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar yadda rubutu yake, da kuma muhimmancinsa. Dole ne ɗalibai su sami damar amfani da littattafai da ire-iren hanyoyin rubutu, domin su saba da amfani da bayanai ta kafofi daban-daban. Wannan hanyar koyo za ta taimaka wa ɗalibai su gane cewa rubutu wakilin magana ne, kuma yana tattare da ma’ana. Rarrafe Koyon Karatu Wannan hanya kai tsaye take tallafa wa bayanin fara aiki daga sananne zuwa ga baƙon aiki. Ta hanyar farawa da rarrafe, ɗalibai za su tinkari sabon aiki da ma’aunin fahimtar da suke da ita. A koyarwa, maimakon jin amsar tambaya kai tsaye, ana tallafa wa ɗalibai su samo amsar da ta yi daidai. Ya kamata a tallafa wa ɗalibai da hanyar ta rarrafe, ta hanyar yi musu gyara. Misali, ɗalibi/ ɗaliba ya yi kuskuren karanta kalmar “yaro”, ya ambaci “yawo”, sai a ce masa, “ka samo sautin farko daidai”. Ko kuma, ɗalibi/ɗaliba da ya nuna jan biro, ya kira shi “baƙin biro”, sai a ce da shi, “haka ne, biro ne. To sai dai baƙi ne, ba ja ba”. Hanyar Koyarwa Ta RARA, tsari ne na jaddadawa da faɗaɗa muhimman rassan da ke dunƙule a cikin Manhajar Hausa ta Hukumar Bincike Da Bunƙasa Ilimi (NERDC 2012). Haka kuma tsarin ya tsamo jigogin rayuwa ta yau da kullum na manhajar, da suka haɗa da bayanin iyali da ciniki da kiwon lafiya da motsa jiki da sufuri da noma da ire-iren ayyukan jama’a, waɗanda a kansu ne aka gina darussan da ke ciki. vii Jagoran Malamai - Aji 2 Gwaji Muhimmancin gwajin bi-da-gyara - A cikin kowane aji za a sami ɗalibai da ke da buƙatu da ƙwarewa da suka sha bamban da juna. Abu ne mai muhimmanci malamai su samar da hanyoyin inganta koyarwarsu domin dukkan ɗaliban su kai ga samun nasara. Gwajin bi-da-gyara zai fayyace wa malamai muhimman bayanai dangane da abin da ɗalibai suka koya, sannan hanyar za ta iya bai wa ɗalibai shawarar gyara aikinsu nan take. Gwajin bi-da-gyara na iya kasancewa da ɗaiɗaikun ɗalibai ko rukuninsu ko kuma da dukkan ɗaliban aji. Ana ba da shawarar yadda gwajin zai kasance a ko’ina cikin Jagoran Malamai, domin tallafawa wajen binciko fahimtar ɗalibai ta yau da kullum, domin bunƙasa cigabansu. Mene ne gwajin bi-da-gyara? Gwajin bi-da-gyara hanya ce mai sauƙi da malamai kan iya binciko fahimtar ɗalibansu. Gwajin-bi-da-gyara kan iya ɗaukar salo iri-iri, waɗanda malamai za su iya amfani da su. A cikin wannan jagora, za a sami misalai ƙarara kan yadda za a gudanar da gwaje-gwajen gano fahimta. Hanyar gwajin bi-da-gyara da aka fi sani ita ce yin tambaya. Malamai na iya amfani da yin tambayoyi domin gano bayanin fahimtar ɗalibai. Kowane darasi da ke cikin jagoran malamai na ƙunshe da rubutattun tambayoyi da ke mai da hankali kan muhimman bayanan da labari ya ƙunsa. Malamai na iya amfani da yin tambaya su binciko fahimtar ɗalibai. Ta hakan, gwajin zai ba da hasken yadda za a tinkari matakin koyarwa na gaba. Wata sananniyar hanyar gwajin bi-da-gyara na faruwa ne lokacin da ɗalibai ke karatu a bayyane: ko a matakin harafi ko na gaɓar kalma ko na kalma ko na jimla. Malamai na iya binciko fahimtar darasi a lokacin da ɗalibai suka mai da hankali ga yin ayyukan da aka ba su a lokuta dabandaban cikin koyar da darasi. Misali, a lokacin da aka nemi dukkan ɗalibai su maimaita karanta wata gaɓar kalma, ko kalma, ko jimla, malami na iya tono zurfin fahimtar ɗalibi. Ta hakan, sai malamai su iya tantance ko lokacin wucewa gaba ya yi, ko kuma sai an maimaita koyarwar. Gwajin bi-da-gyara a matsayin tsarin koyarwa na yau da kullum - Akwai hanyoyin gwajin bi-da-gyara da dama a cikin tsarin darasinka da ke cikin jagoran malamai. Kowane darasi an raba shi gida biyar: fahimtar ƙwayoyin sauti da tsarin haruffan harshe da kalmomi da iya karatu da fahimta. Sannan kuma kowane reshe daga cikin waɗannan yana da jerin ayyuka uku: ‘In Yi, Mu Yi, Ku yi.’ Da farko malami zai yi dukkan abin da yake son a kwaikwaya. A aiki na ‘Mu Yi, ana sakin ragamar koyarwar ne a hankali, don mai da koyo a hannun ɗalibi. A aikin ‘Ku Yi’ kuwa, ɗalibai za su sami damar nuna ƙwarewarsu a fannin da aka koya musu. A cikin ayyuka biyu na ƙarshen darasi ne malami ke da damar binciko fahimtar ɗalibansa. Misali, a sashen darasin da ke koyar da Fahimtar ƙwayoyin Sauti, za a nemi ɗalibai su ‘Tafa Kalma’. Malami zai nemi dukkan ɗalibai su furta kalma, su kuma tafa ta. Ta hakan, malami zai sami damar duddubawa ya ga ɗaliban da ba sa aikin furuci da tafawa tare da sauran ɗalibai. Ka ga malami na da ƙarin samun damar binciko fahimta, ta hanyar tambayar ɗalibai su nuna ƙwarewarsu wajen tafa gaɓoɓin kalma su kaɗai. Malamai yana ba da damar ƙara horuwa a dukkan sassan a lokacin darasi na biyu cikin mako. Ana son malamai su karkato darasin na biyu a cikin mako zuwa samun ƙarin ƙwarewar ɗalibai a kan sassan nan biyar da ke cikin kowane darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti, Tsarin Haruffan Harshe, Iya Karatu, Kalmomi, da Fahimta. Jagoran Jagoran Malamai - Aji 2 viii Gwajin Jagorancin Koyarwa Gano abin da ɗalibai suka sani tun farko Gano fahimta - wucewa zuwa wani bayani, ko a maimaita koyarwa Koyar da bayani Koyar da bayani na gaba, ko a maimaita koyarwa Binciko fahimtar bayani Da’irar Auna Fahimta Da’irar tana farawa da auna abin da ɗalibai suka sani ko suka fahimta a baya. A kowane mataki na batun da aka koyar, ya kamata malami ya auna fahimtar ɗalibai, don gano ko sun fahimci abin da aka koya musu. Idan ba su fahimta ba, sai a sake bitar batun sannan a sake auna fahimtarsu. ix Jagoran Malamai - Aji 2 Ƙa’idojin Amfani da Allo 1. Da zarar malamai sun shiga aji, su tabbatar an kawar da duk wani abu da ba shi da alaƙa da darasin da za su gabatar. 2. A raba allon gida biyu don jin daɗin rubuta bayanai ko kayan aiki. 3. Malamai za su fara rubutu a allo daga hagu zuwa dama 4. Malami/ma ya/ta tsaya gefe idan yana rubutu a allo. Kada malami/ma ya/ta riƙa magana da allo, ya/ta juya wa aji baya. 5. Malami/ma zai/za ta yi wa aji bayani yana kallon ɗalibai, sannan ya koma gefe ya yi rubutu a allo. 6. Rubutu a allo ya kasance mai kyau kuma mai karantuwa. 7. Kada bayanai ko kayan aiki su yi yawa a allo 8. A riƙa goge allo da dasta, kodayaushe. 9. Malamai su riƙa duba bayanan da suka rubuta ko kayan aiki, idan sun ga wani kuskure su gyara 10. Malamai na iya sa ɗalibai yin wani aiki a kan allo Jagoran Malamai - Aji 2 x Dabarun Iya Rubutu Kula da sigar harafi: Yana da muhimmanci ɗalibai su naƙalci yanayin kowane harafi. Da zarar ɗalibai sun naƙalci yanayin harafi, to sai a jawo hankalinsu wajen yadda ake ƙawata su da rubuta su dalla-dalla, musamman dangantakar harafi da layukan da ke kan takarda. Lura da yadda ake rubuta harafi: A yayin kowane rubutu, haruffa na kasancewa ne a ƙasan layi a tsakanin layuka biyu. Manya haruffa ana rubuta su ta hanyar cika tsakanin layukan da su. Su kuwa ƙananan haruffa wasu kan sami layin da zai cika daga sama (b, d, h i), wasu kuma wutsiyarsu daga ƙasa kan ƙetara har layin da ke ƙasa (g, j, y), amma mafi yawansu na tsayawa a tsaka-tsakin layukan nan biyu. Da zarar ka gabatar da sabon harafi, to sai ka danganta shi da bayanan da muka yi a baya dangane da layukan nan biyu, kodayake ba dole ba ne ɗalibai su kiyaye da wannan ƙai’dar, har sai sun gama naƙaltar yanayinsu. A wannan lokacin sai ka jawo hankalinsu a kan wannan ƙai’dar. Yanayin zama da aje takarda da riƙon fensiri Za a fara da nuna wa ɗalibai yadda za su riƙe fensiri daidai. Ana son su sanya fensirin tsakanin yatsu uku (babban yatsa da manuniya da kuma na tsakiya). Babban yatsa shi ne gefe, manuniya na sama, shi kuma na tsakiya yana daga ƙasa ya tare fensir. A ɗan karkata fensirin kaɗan. A duk lokacin koyon rubutu, musamman a darussan farko-farko, ana iya koya wa ɗalibai waƙa kamar haka: Babban ɗan yatsa gefe, Manuniya ko na sama, Ɗan tsakiya kuma na ta ƙasa. Bayan an gama rera waƙar sai a sanyasu su riƙe tare da ɗaga fensirinsu sama kana/kina kewayawa don ganin yadda suka riƙe shi. A tabbatar ɗalibai sun ba da ‘yar tazara tsakanin yadda suke zaune da tebirinsu, yadda za su iya aza hannunsu a kan tebiri cikin jin daɗi da natsuwa. Badaman ɗalibai su aje takardarsu a kusurwa daga dama. Bahagun ɗalibai kuma su aje takardunsu a kusurwa daga hagu. xi Jagoran Malamai - Aji 2 Alamomi Aikin Malami/Malama: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi. Aikin Malami/Malama da Ɗalibai: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa. Aikin Ɗalibai: A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu. Alamar Akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar ta akwati. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar akwati da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar ta da’ira. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar ta dala. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar dala da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar ta tauraro. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/ za ta ɗauka domin karantar da sashe. Jagoran Malamai - Aji 2 xii ZANGO NA 1 Mako 1 - 8 Darasi 1 - 16 1 Jagoran Malamai - Aji 2 Manufar Malamai da Ɗalibai Zango na 1 Manufar Malamai Manufar Ɗalibai Jigo na 1 Iyali A ƙarshen wannan sashe, malamai za su san ginshiƙan abubuwa na koyar da karatu ga ‘yan azuzuwan farko da muhimmancinsu: A wannan sashe za a gabatar da iyalan gidan su Nana ga ɗalibai. • • • • Mako na 1-4 Fahimtar Ƙwayoyin sauti: Sauraran sautuka a cikin harshe. Tsarin Haruffan Harshe: Fahimtar dangantakar da ke tsakanin harafi da sauti. Iya Karatu: Iya karanta jimla da labari. Sabbobin Kalmomi da Fahimta: Karatu tare da fahimtar abin da aka karanta tare da bayar da amsar tambayoyi. A ƙarshen mako na 1-4 , ana son malamai su san: Ƙwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karanta su da kuma ƙwazonsu wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • Mako na 1: ‘N’ ‘n’ ‘A’ ‘a’ ‘ • Mako na 2: K’ ‘k’ ‘A’ ‘a’ • Mako na 3: ‘M’ ‘m’ ‘A’ ‘a’ • Mako na 4: ‘S’ ‘s’ ‘A’ ‘a’ Ƙwazon ɗalibai a wajen iya: • karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. • Yi wa ɗalibai tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi da tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Shawara a kan Gwaji A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘N’ ‘K’ ‘M’ ‘S’ da wasalin ‘A’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: • Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. • Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace Jagoran Malamai - Aji 2 2 Malamai za su taimaka wa ɗalibai don su iya danganta abubuwan da suka sani a gidajensu ta hanyar karanta labarai a kan gidan su Nana A ƙarshen mako na 1-4, ana son ɗalibai su iya: Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 1: ‘N’ ‘n’ ‘A’ ‘a’ ‘ Mako na 2: K’ ‘k’ ‘A’ ‘a’ Mako na 3: ‘M’ ‘m’ ‘A’ ‘a’ Mako na 4: ‘S’ ‘s’ ‘A’ ‘a’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Bayar da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Zango na 1 Manufar Malamai Manufar Ɗalibai Jigo na 2 Muhalli A ƙarshen wannan sashe, malamai za su san ginshiƙan abubuwa na koyar da karatu ga ‘yan azuzuwan farko da muhimmancinsu: A wannan sashe za a gabatar da iyalan gidan su Nana ga ɗalibai. • • • • Mako na 5-8 Fahimtar Ƙwayoyin sauti: Sauraran sautuka a cikin harshe. Tsarin Haruffan Harshe: Fahimtar dangantakar da ke tsakanin harafi da sauti. Iya Karatu: Iya karanta jimla da labari. Sabobbin Kalmomi da Fahimta: Karatu tare da fahimtar abin da aka karanta tare da bayar da amsar tambayoyi. A ƙarshen mako na 5-8, ana son malamai su: San kwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karantasu da kuma ƙwazonsu su a wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 5:‘R’ ‘r’ ‘I’ ‘i’ Mako na 6: ‘D’ ‘d’ ‘I’ ‘i’ Mako na 7: ‘T’ ‘t’ ‘I’ ‘i’ Mako na 8: ‘Ts’ ‘ts’ ‘I’ ‘i’ San ƙwazon ɗalibai a wajen iya karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. Shawara a kan Gwaji Malamai za su taimaka wa ɗalibai don su iya danganta abubuwan da suka sani a gidajensu ta hanyar karanta labarai a kan gidan su Nana A ƙarshen mako na 5-8, ana son ɗalibai su iya: Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 5: ‘R’ ‘r’ ‘I’ ‘i’ Mako na 6: ‘D’ ‘d’ ‘I’ ‘i’ Mako na 7: ‘T’ ‘t’ ‘I’ ‘i’ Mako na 8: ‘Ts’ ‘ts’ ‘I’ ‘i’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Yi wa ɗalibai tambayo uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Bayar da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙe ‘R’ ‘D’ ‘T’ ‘Ts’ da wasalin ‘I’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: • Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. • Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace 3 A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Kafin Darasi Waƙa 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gai da iyayenmu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [Nana]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [Nafisa, nama, noma]. Aikin Malami: Jagoran Malamai - Aji 2 4 Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 1Q $D QD DQQDQ 1DQDQDDQD 1DQDQDJLGD 1Q1Q1Q $D$D$D 1D$QQDQ .DUDWXQODEDUL 1DQDQDQDQ 1DQDQDJLGD 1DQDQDZDVDQJDODJDOD Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [N n]. Minti-6 6.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [N], sautinsa /n/.” 7. Maimaita mataki na shida (6) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 8. Maimaita mataki na farko zuwa na huɗu(1-4) da ɗaya harafin [A a]. 3.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na biyu (2) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 9. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 4. Maimaita mataki na uku (3) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 5. Koya wa ɗalibai furta sautin [N] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[N] na da sautin /n/ kamar a cikin kalmar noma.” Ka/ki kwatanta yadda ake noma kana/kina furta sautin ‘n’ ‘n’ ‘noma. 10. Maimaita mataki na shida da na bakwai (6-7). 11. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [N, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 5 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 1 Gano Gaɓar Kalma 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [na]. Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [an, nan]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalma [Nana] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita aikin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita aikin tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 1 da Na 2 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [na, ana]. 6 Zango Na: 1 Karatun Jimla Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na gida]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [gida]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. Nana na nan. Nana na gida. Nana na wasan gala-gala. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da littafin Karatun ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. Karatun Labari A Bayyane 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 7 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Minti-5 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 2 a cikin Littafin Karatu A Bayanne. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙabila, rana]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Nn, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa, ko a bayan wani ɗalibi/ɗaliba da suke tare. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 8 Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darussan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti. Aiki: Bambanta Sautuka. Manufa: Yi gwajin gano ko ɗalibai na iya bambantawa tsakanin sautin farko da na ƙarshe. Tsari:Faɗi kalmomi biyu. Nemi ɗalibai su faɗa maka/maki sautukan farko da na ƙarshe na kalmomin ɗaya ne. Shawara Matashiya A Kan Darasi Na 2 Rubuta waƙar kan babbar takarda na taimaka wa ɗalibai wajen rera waƙar. Ana iya amfani da bayan kalandu, da manyan kwalaye wajen rubuta waƙar. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 3 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [zaune, tebur]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [2] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Wane bangare na darasi ɗalibai suka fi fahimta? Me ya sa ka/ki ke ganin ka/kin shirya wa wannan darasi? Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin ya kamata a canza cikin waɗannan abubuwa? 9 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [kaka]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [kaza, kakaki, kare]. in Malami: Jagoran Malamai - Aji 2 10 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 .N $D ND QD NDNDNDQDQDND .DNDQDPDVD .N.N.N $D$D$D .D$NND .DUDWXQODEDUL .DNDQDJLGD .DNDQDPDVD 1DQDQDNDOOR Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [N, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 hannunka/ki na dama kana/kina kama na hagu kana/kina furta sautin ‘k’ ‘k’ ‘kama’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [K k]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [K], sautinsa /k/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na hudu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [K] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[K] na da sautin /k/ kamar a cikin kalmar kama.” Ka/ki yi amfani da 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [K, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 11 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Gano Gaɓar Kalma Darasi Na 3 da Na 4 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ka]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [na]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [kaka] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [kana, naka]. 12 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Karatun Jimla Darasi Na 3 da Na 4 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Kaka na masa]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [masa]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Kaka na gida. Kaka na masa. Nana na kallo. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 13 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 3 da Na 4 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 4 a cikin Littafin Karatu A Bayanne. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [Ƙofa, bishiya]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayanne. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Kk, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 14 Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti. Aiki: Ɗaga Hannu Taɓo Tauraro. Manufa: Yi gwajin fahimtar ɗalibai wajen sauraron sautukan kalamomi. Tsari:Nemi ɗalibai su tashi tsaye. Malami/Malama zai/za ta faɗi kalma. Su kuma ɗalibai za su yi kamar suna kan cafko tauraro daga sama, a kowane sauti ko gaɓa a sheɗara ko jimla. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Lura da fahimtar ɗalibai: Zaɓi yara biyar da za ka lura da aikinsu tun da farko. Idan 4 ko 5 na iya tafa kalmomi daidai, to ka ci gaba. Idan 3 ko 4 ne kawai ke iyawa, to a maimaita aikin. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 5 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [marainiya, ladabi]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [4] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Ko ɗalibai sun ji daɗin waƙar da kuma motsa jikin da ake yi a cikinta? Saboda me? Ko ka/kin shirya wa aiwatar da waƙa kafin shiga aji? I ko a’a me ya sa? Bayan waiwaye me ka/ki ke tunanin za ka/ki canza don koyar da waƙa sosai. 15 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gai da iyayenmu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [masa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [mama, masara, makaranta]. Jagoran Malamai - Aji 2 16 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 0P $D PD DPQD PDPDDPPDQDPD 0DPDQDFLQQDPD 0P0P0P $D$D$D 0D$PPD .DUDWXQODEDUL 0DPDQDJLGD 0DPDQDFLQQDPD 1DQDQDPDVD Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 da miƙa wuyanka/ki gaba kana/kina furta sautin ‘m’ ‘m’ ‘mmoow’. 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [K, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [M, m]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [M], sautinsa /m/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a]. 10.Koyawa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [M] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[M] na da sautin /m/ kamar a cikin kukan Saniya.” Ka/ki rinƙa ɗagawa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [M, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 17 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ma]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [am, na]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [mama] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 5 da Na 6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [amma, nama]. 18 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Karatun Jimla Darasi Na 5 da Na 6 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Mama na cin nama]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cin]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. Mama na gida. Mama na cin nama. Nana na masa. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 19 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Karatun Labari A Bayyane 1.Buɗa shafi na 6 a cikin littafin karatu a bayyane. Darasi Na 5 da Na 6 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kogi, tsoro]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/ki ka karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Mm, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 20 Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na bukatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 6 a Littafin Karatu A Bayyane. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara A kwaɗaita wa ɗalibai son gano keɓaɓɓun kalmomin darasin ‘Tafa Kalma’ da ke haɗe da hoto a cikin littafin. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 7 a Littafin Karatu a Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [gwala-gwalai, mamaki]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [6] a cikin Littafin Karatu a Bayyane. Me yasa ka/ki ke ganin yawancin ɗalibai sun tafa kalmomin daidai? Me ka/ki ke ganin ya sa ka/kin ci nasarar koyar da wannan sashe na darasin? Bayan waiwaye me ka/ki ke tunanin za ka/ki canza don koyar da tafa gaɓar kalma. 21 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗalibai ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [saƙa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [sanda, saniya, sarauniya]. Jagoran Malamai - Aji 2 22 Zango Na: 1 Mako Na: 4 6V Darasi Na 7 da Na 8 $D VD PDQD NDVDVDPD QDVD 1DQDQDVDǎD 6V6V6V $D$D$D 6D$VVD .DUDWXQODEDUL 1DQDQDVDǎD 1DQDWDVDǎDKXOD +XODQDVDPDQWHEXU Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [M, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [S s]. Minti-6 hannuwa kamar kana/kina saƙa kana/kina furta sautin ‘s’ ‘s’ ‘saƙa’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [S], sautinsa /s/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [S] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[S] na da sautin /s/ kamar a cikin kalmar saƙa.” Ka/ki riƙa lanƙwasa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [S, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 23 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 4 Gano Gaɓar Kalma Darasi Na 7 da Na 8 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [sa]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ma, na]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [kasa] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [sama, nasa]. Karatun Jumla Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-6 24 Zango Na: 1 Karatun Jimla Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na saƙa]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [saƙa]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Nana na saƙa. Nana ta saƙa hula. Hula na saman tebur. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 25 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 4 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 7 da Na 8 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kake karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sababbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 8 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kwaɗayi, gunaguni]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ss, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 26 Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na bukatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Tsarin Baƙaƙe. Aiki: Tono Kalma. Manufa: Zai jaddada sanin baƙaƙe a rubutu. Tsari:A ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen bin ba’asin ɗaiɗaikun baƙaƙe da kalmomi da aka gabatar musu da su a cikin darasi, waɗanda suke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Yi amfani da azancin maganar hannu, kamar ɗaga yatsa wajen ba ɗalibai dama don su ba da amsa tare da kuma yi musu gyara a inda suka yi kuskure. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 9 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [faɗi, juya]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [8] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Wane taimako ne jami’an taimaka wa malamai ya baka/ki a cikin darussan da suka gabata? A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’an taimaka wa malamai? Ko kana da jami’an da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/ki ke so jami’an su tattauna a lokacin taro malamai na gaba. 27 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Wanke hannu yara shi ne tsafta Tsafta Wanke baki yara shi ne tsafta Tsafta Wanka, wanki yara shi ne tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [rana]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [rigima, rijiya, riga]. Jagoran Malamai - Aji 2 28 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 5U,L UDUL ULQDUDQDULQL 1DQDQDULQDULJD 55UU5U ,L,,L, 5L,UL5 .DUDWXQODEDUL 5DQDWDÀWR 1DQDQDULQDULJD $PLQDQDULQDULJD Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [S, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 kalmar rawa.” Ka/ki ɗan yi ‘yar rawa kana/kina furta sautin ‘r’ ‘r’ ‘rawa’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [R, r]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [R], sautinsa /r/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [R] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[R] na da sautin /r/ kamar a cikin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [R, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 29 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ra]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ri]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [rina] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 9 da Na 10 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [rana, rini]. 30 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Karatun Jimla Darasi Na 9 da Na 10 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na rina riga]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [riga]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Rana ta fito. Nana na rina riga. Amina na rina riga. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 31 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Karatun Labari A Bayyane 1.Buɗa shafi na 10 a cikin littafin karatu a bayyane. Darasi Na 9 da Na 10 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [girmama, yafe]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Rr, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 32 Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafin su. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Gwanewa. Aiki: Tusa Karatu. Manufa: Tusa karatun labari sau da dama, domin ɗalibai su haɓaka gwanewarsu ta hanyar ƙara ganin kalmomi da kuma aiki da su. Tsari: Sa su su tusa karatu sau da dama, sannan a dubi halin fahimtarsu. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Manufar ita ce a samu ɗalibai su iya karanta kalmomi 9 cikin 10 babu kuskure. Idan ɗalibai sun kasa samun maki 90% a karatun, to a sa su, su yi ta maimaita jimlar don samun ƙwarewa. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 11 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [rassa, tsallake]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [10] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Ko sun gane/ba su gane sunayen haruffa da sautin su ba? Waɗanne ɓangarori ne suke ba ka/ki matsala wajen koyar da sunayen haruffa da sautinsu? Me za ka/ki canza a cikin darasin bayan waiwaye? 33 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [daka]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [Ladi, dila, dillali]. Jagoran Malamai - Aji 2 34 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 'G,L GLGDPL GDPLQDGDPLGDND 1DQDQDJ\DUDGDPL 'GG'G' ,L,,L, 'L,GL, .DUDWXQODEDUL .DNDQDGDNDGDZD 1DQDQDJ\DUDGDPL 6DLJDPDJH Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [R, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 sako su kamar mai daka, kana/kina furta sautin ‘d’ ‘d’ ‘daka’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [D, d]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [D], sautinsa /d/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i” ‘i” ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [D] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[D] na da sautin /d/ kamar a cikin kalmar daka.” Ka/ki riƙa ɗaga hannuwanka/ki sama kana/kina 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [D, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 35 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [di]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [da, mi]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [damina] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 11 da Na 12 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [dami, daka]. 36 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Karatun Jimla Darasi Na 11 da Na 12 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na gyara dami]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [gyara]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. Kaka na daka dawa. Nana na gyara dami. Sai ga mage. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 37 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 11 da Na 12 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 12 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [reshe, danƙo]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jikinka, ko kuma hotuna. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Dd, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 38 Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafin su. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Gwanewa. Aiki: Karatun Tare. Manufa: Yi amfani da tusa karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su ƙwarin gwiwa. Tsari:Haɗa ɗalibai, sannan ka tsamo labarin da za su yi aiki a kai. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Karatun Amsa Amo: Nemi ɗalibai su karanta kalma ko jimla bayan ka/kin karanta don gano ƙwarewarsu. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 13 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [dabara, ankara]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [12] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Ko kana ganin motsin sautuka sun yi sauƙi/tsauri ga ɗalibai? Saboda me ka/ki ke ganin koyar da motsin sautuka ya yi sauƙi/ wuya? Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin zaku tattauna da abokan aikin ka/ki a wurin taron malamai? 39 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Kafin Darasi Darasi Na 13 da Na 14 Waƙa 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gaida iyayen mu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [dafi]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [takalmi, titi, turmi]. Jagoran Malamai - Aji 2 40 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 7W,L WLWD PDWDWLWLWDVD 7DQDULǎHGDWDVD 7W7W ,L,L 7L,W,L .DUDWXQODEDUL .DNDQDNDQWDEDUPD 1DQDQDNDQWXUPL 7DQDULǎHGDWDVD Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [D, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 hannuwanka/ki kana/kina furta sautin ‘t’ ‘t’ ‘tafi’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [T t]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [T], sautinsa /t/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [T] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[T] na da sautin /t/ kamar a cikin kalmar tafi.” Ka/ki riƙa tafa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [T, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 41 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ti]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ta]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [mata] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 13 da Na 14 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [titi, tasa]. 42 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Karatun Jimla Darasi Na 13 da Na 14 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [tana riƙe da tasa]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [riƙe]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. Kaka na kan tabarma. Nana na kan turmi. Tana riƙe da tasa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin yara dabandaban. 43 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 13 da Na 14 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 14 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [muhalli, mamaki]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Tt, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 44 Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 Aikin Gida 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Karatun Tare. Manufa: Yi amfani da tusa karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su ƙwarin gwiwa. Tsari:Nemi ɗalibi ɗaya ya karanta labarin sau uku - shi kuma ɗaya ya yi bayani a kan abu guda da ya karanta sosai, da kuma ɗaya wanda zai gyara a gaba. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Faɗaɗa kalmomi yana da alaƙa da ƙwarewa wajen karatu. A koyar da ma’anar kalmomi, da jimlolinsu, da labarin da suka ƙunsa. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 15 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [dabbobi, halaka]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [14] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Ko kana ganin ɗaliban ka/ki suna iya/ ba su iya rubuta haruffa daidai? Me ya sa? Wace matsala ka/ki ke fuskanta wurin koyar da rubutu? Bayan waiwaye wace dabara za ka/ki canza wajen koyar da rubutu? 45 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Waƙa Kafin Darasi 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. Waƙar Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Wanke hannu yara shi ne tsafta Tsafta Wanke baki yara shi ne tsafta Tsafta Wanka, wanki yara shi ne tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [tsafta]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [motsi, hatsi, tsintsiya]. Jagoran Malamai - Aji 2 46 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 7VWV,L WVDWVLQL WVDNDQLWVLQNDWVDQDQL $EEDQDGDWVDQDQLQWVDIWD .DUDWXQODEDUL 7VWV7VWV ,L,,L, 7V,LWVL $EEDQDGDWVLQWVL\D $EEDQDVKDUD $EEDQDGDWVDQDQLQWVDIWD Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [T, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 hankali kana/kina furta sautin ‘ts’ ‘ts’ ‘tsalle’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ts ts]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ts], sautinsa /ts/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ts] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ts] na da sautin /ts/ kamar a cikin kalmar tsalle.” Ka/ki riƙa yin tsalle a 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ts, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 47 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [tsa]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [tsi, ni]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [tsakani] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 15 da Na 16 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [tsinka, tsanani]. 48 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Karatun Jimla Darasi Na 15 da Na 16 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Abba na da tsananin tsafta]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [tsafta]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. Abba na da tsintsiya. Abba na shara. Abba na da tsananin tsafta. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 49 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 15 da Na 16 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sababbin kalmomin. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 1.Buɗa shafi na 16 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [samaniya, tashi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ts, ts, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 50 Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Tusa Karatu. Manufa: Tusa karatun labari sau da dama, domin ɗalibai su haɓaka gwanewarsu ta hanyar daɗa ganin kalmomi da kuma aiki da su. Tsari:Faɗa wa ɗalibai cewa suna karanta labarin ne don su ƙara goguwa wajen karatu, da sanin kalmomi, da muhallinsu, da kuma karanta kalma ba da garaje ba. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Yi amfani da ‘yar takarda mai ɗauke da keɓaɓɓun kalmomi uku da aka koya, don tantance azancin kowane ɗalabi/ɗalaba na tsamo kalmomin a lokacin da suke karatu da kansu. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 17 a Littafin Karatu a Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [hikima, sulhi]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [16] a cikin Littafin Karatu a Bayyane. Wane taimako ne jami’in/ar taimaka wa malamai ya/ta baka a cikin darussan da suka gabata? A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’ian taimaka wa malamai? Ko kana da jami’in/ar da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/ki ke so jami’ian su tattauna a lokacin taron malamai na gaba. 51 Jagoran Malamai - Aji 2 Alamomi Aikin Malami/Malama: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi. Aikin Malami/Malama da Ɗalibai: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa. Aikin Ɗalibai: A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu. Alamar Akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar ta akwati. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar akwati da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar ta da’ira. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar ta dala. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar dala da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar ta tauraro. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/ za ta ɗauka domin karantar da sashe. Jagoran Malamai - Aji 2 52 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 ZANGO NA 2 Mako 1 - 8 Darasi 1 - 16 53 Jagoran Malamai - Aji 2 Manufar Malamai da Ɗalibai Zango na 2 Manufar Malamai Manufar Ɗalibai Jigo na 3 Filin Wasa A ƙarshen wannan sashe, malamai za su iya kula da fahimtar ɗalibansu ta hanyar amfani da takardar bayani wajen: A wannan sashe, an gabatar da hanyoyin motsa jiki a makaranta da dandali. • • • • • • Mako na 1-4 Tafa gaɓobin da ke cikin kalma Faɗar sunan harafi da sautinsa Karanta kalmomi da jimlolin da ake buƙata Karanta labari tare da ba da amsar tambayoyi Rubuta haruffan da ake buƙata Sauraren labari tare da amsa tambayoyi aƙalla uku. A ƙarshen mako na 1-4 , ana son malamai su: A ƙarshen mako na 1-4 , ana son ɗalibai su iya: San ƙwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karantasu da kuma ƙwazonsu su a wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 1: ‘B’ ‘b’ ‘A’ ‘a’ Mako na 2: ‘W’ ‘w’ ‘A’ ‘a’ Mako na 3: ‘G’ ‘g’ ‘I’ ‘i’ Mako na 4: ‘Y’ ‘y’ ‘I’ ‘i’ San ƙwazon ɗalibai a wajen iya karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. Yi wa ɗalibai tambayo uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Shawara a kan Gwaji A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘B’ ‘W’ ‘G’ ‘Y’ da wasulan ‘A’ ‘I’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: • Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. • Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace Jagoran Malamai - Aji 2 Malamai za su taimaka wa ɗalibai wajen dangantawa da bambanta irin wasannin da suke yi da waɗanda su Nana ke yi. 54 Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 1: ‘B’ ‘b’ ‘A’ ‘a’ Mako na 2: ‘W’ ‘w’ ‘A’ ‘a’ Mako na 3: ‘G’ ‘g’ ‘I’ ‘i’ Mako na 4: ‘Y’ ‘y’ ‘I’ ‘i’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Ba da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Zango na 2 Manufar Malamai Manufar Ɗalibai Jigo na 4 Aji A ƙarshen wannan sashe, malamai su gano ɗaliban da suke samun matsala wajen karatu da rubutu sannan a shirya musu darussa na musamman a kan waɗannan ɓangarori: A wannan sashe, an gabatar wa ɗalibai abubuwan da Nana da Abba ke yi a makaranta. • • • • Mako na 5-8 Fahimtar Ƙwayoyin Sauti: Bambance sautukan haruffa Karatu: Iya karanta gaɓar kalma da kalmomin da ake buƙata. Iya Karatu: Yin karatu cikin hanzari kamar yadda ya dace tare da kakkarya murya. Fahimta: Fahimtar labarin da aka karanta ta hanyar amsa tambayoyin da ke cikin labarin. A ƙarshen mako na 5-8, ana son malamai su: San ƙwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karantasu da kuma ƙwazonsu su a wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 5: ‘L’ ‘l’ ‘U’ ‘u’ Mako na 6: ‘C’ ‘c’ ‘I’ ‘i’ Mako na 7: ‘H’ ‘h’ ‘U’ ‘u’ Mako na 8: ‘Sh’ ‘sh’ ‘I’ ‘i’ San ƙwazon ɗalibai a wajen iya karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. San yi wa ɗalibai tambayo uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi. Shawara a kan Gwaji A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘L’ ‘C’ ‘H’ ‘Sh’ da wasulan ‘I’ ‘U’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: • Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. • Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace 55 Malamai za su taimaka wa ɗalibai wajen danganta abubuwan da suke yi a makaranta da na su Nana da Abba. A ƙarshen mako na 5-8, ana son ɗalibai su iya: Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 5: ‘L’ ‘l’ ‘U’ ‘u’ Mako na 6: ‘C’ ‘c’ ‘I’ ‘i’ Mako na 7: ‘H’ ‘h’ ‘U’ ‘u’ Mako na 8: ‘Sh’ ‘sh’ ‘I’ ‘i’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Ba da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gaida iyayenmu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [baba]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [babba, bishiya, dabara]. Jagoran Malamai - Aji 2 56 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 %E $D ED EDEQL EDEDEDEEDEDEDQD %DEDGD$EEDQDZDVD %E%E%E $D$D$D %DE%DE .DUDWXQODEDUL $EEDDEDEEDQÀOL %DEDGD$EEDQDZDVD 1DQDGD$PLQDQDZDVD .RZDQDZDVDDÀOL Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ts, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 murɗa hannun babur ɗin kana/kina furta sautin ‘b’ ‘b’ ‘boom-boom’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [B b]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [B], sautinsa /b/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [B] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[B] na da sautin /b/ kamar a cikin kukan babur.” Ka/ki nuna alamar kana/kina kan babur kana/kina 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [B, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 57 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ba]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [bab, ni]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [baba] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 1 da Na 2 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [babba, babana]. 58 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Karatun Jimla Darasi Na 1 da Na 2 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Baba da Abba na wasa]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [wasa]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 4. Rubuta labarin a kan allo. Abba a babban fili. Baba da Abba na wasa. Nana da Amina na wasa. Kowa na wasa a fili. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 59 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 1 da Na 2 4.Nemi ɗalibai su mai da hankali kan gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 19 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [hantsi, birni]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Bb, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 60 Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Koyon Sabuwar Kalma. Manufa:Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen makaranta. Tsari:Keɓe minti ɗaya ko biyu a mako domin samun jin bayanin yadda ɗalibai suka tsinci kalma, da kuma ma’anarta. Nemi ɗalibai su fito su rubuta kalmominsu a kan allo. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Ba su dama su furta kalmomi, tare da jinsu a cikin waƙa yana haɓaka fahimtarsu ta sauraro da gina kalmomi. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 20 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [abokinsa, buhuna]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [19] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Me ka fahimci yawancin ɗalibai suka fi so ? Me ka fi jin daɗin koyarwa a cikin darasinka ? Bayan waiwaye waɗanne sassa ne ka/ki ke jin kana iya koyarwa yau ? 61 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Kirge Ɗaya mafarin ƙirge Biyu idanun dabba Uku duwatsun murhu Huɗu ƙafafun tebur Biyar na yatsun hannu. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [wake]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [wanka, rawa, taimakawa]. Jagoran Malamai - Aji 2 62 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 :Z $D ZD VDVDQ ZDVDZDWDZDQND 1DQDWD\LZDQND :Z:Z $D$D$D :D$ZD .DUDWXQODEDUL -L\DDQJDZDWDQ6DOODK 1DQDWD\LZDQND 1DQDGD$PLQDQDUDZD $QDZDVDQVDOODK Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [B, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 watsa ruwa da cuɗawa kana/kina furta sautin ‘w’ ‘w’ ‘wanka.’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [W w]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [W], sautinsa /w/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [W] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[W] na da sautin /w/ kamar a cikin kalmar wanka.” Ka/ki kwatanta 63 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [W, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [wa]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [sa, san]. Kalmomin da Za A karanta 1. Rubuta wannan kalmar [wasa] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 3 da Na 4 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [wata, wanka]. 64 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Karatun Jimla Darasi Na 3 da Na 4 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana ta yi wanka]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [yi]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Rubuta labarin a kan allo. Jiya an ga watan sallah. Nana ta yi wanka. Nana da Amina na rawa. Ana wasan sallah. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 65 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 3 da Na 4 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 21 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [fushi, dace]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ww, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 66 Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Koyon Sabuwar Kalma. Manufa:Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen makaranta. Tsari: Samar da waje, ko allon manna sabbin kalmomi. Shawara Matashiya A Kan Darasi Na 2 A sa ɗalibai su yi hasashen ma’anar kalmomi, sannan a saurari bayaninsu don tabbatar da hasashensu. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 22 a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [wahala, wurare]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [21] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Me ka gano ɗaliban ka sun fi ƙwarewa a wajen koyon sunayen haruffa da sautukansu? A ina ka/kike da matsala a wajen koyar da sunayen haruffa da sautukansu? Bayan waiwaye me ka/kike ganin ya kamata ka/ki canza wajen koyar da sunayen haruffa da sautukansu? 67 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [gari]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ganga, gatari, gajimarai]. Jagoran Malamai - Aji 2 68 Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 *J,L JLJDQGDQ 5LQJLPLJDVDJDQJD $QDJDVDUNRNDZDD 5LQJLPL .DUDWXQODEDUL *J*J* ,L,,L, *L,JL, $QDJDVDUNRNDZDD5LQJLPL $QDEXJDJDQJD $JLGDQVX$OLDNZDLJDQJD $EEDQDJDVDUNRNDZD Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [W, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 gudu kaɗan kaɗan kana/kina furta sautin ‘g’ ‘g’ ‘gudu’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [G g]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [G], sautinsa /g/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar(2- 5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [G] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[G] na da sautin /g/ kamar a cikin kalmar gudu.” ka/ki kwatanta yin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [G, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 69 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 3 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [gi]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [gan, dan]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [Ringimi] a kan allo Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 5 da Na 6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [gasa, ganga]. 70 Zango Na: 2 Karatun Jimla Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Ana gasar kokawa a Ringimi]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [kokawa]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. Ana gasar kokawa a Ringimi. Ana buga ganga. A gidan su Ali akwai ganga. Abba na gasar kokawa. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 71 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 3 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 5 da Na 6 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 23 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gada, kwale-kwale]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Gg, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 72 Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau ga iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma. Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi. Tsari: Malami/ma zai/zata rubuta kalma a kan takarda. Shawara Matashiya A Kan Darasi Na 2 Sanya ɗalibai su ba da labarin abin da suka karanta yana bai wa malamai damar gano fahimtarsu. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 24 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [giwa, teku]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [23] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Me za ka/ki iya cewa game da ɗalibanka/ki wajen koyon motsin jikin da aka danganta da suna da sautin harafi? Wace matsala ce ka/kika fuskanta wajen motsin jikin da aka danganta da suna da sautin harafi? Wace buƙata ce za ka/ki zo da ita wajen taron malamai a kan darasi don tattaunawa? 73 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Kirge Daya mafarin ƙirge Biyu idanun dabba Uku duwatsun murhu Huɗu ƙafafun tebur Biyar na yatsun hannu. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon sautin gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [yau]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [rairayi, tsautsayi, matambayi]. Jagoran Malamai - Aji 2 74 Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 <\,L \L\DZD \D\LL\D\DZD .DUDWXQODEDUL 1DQDWDL\DNZDOOL\D <DXPDDQDELNLQVDOODK $EEDQD\DZRQVDOODK 1DQDWDL\DNZDOOL\D $PLQDPDWDL\DNZDOOL\D 6XQVDQ\DND\DQ\D\L <\<\< ,L,,L, <L,\L, Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [G, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 kana/kina yanka ɗayan hannun kana/kina furta sautin ‘y’ ‘y’ ‘yanka’ 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Y y]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Y], sautinsa /y/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido.’ 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Y] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Y] na da sautin /y/ kamar a cikin kalmar yanka.” Ka/ki yi amfani da hannunka/ki a matsayin wuƙa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Y, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 75 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 4 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [yi]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ya, wa]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [yayi] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 7 da Na 8 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [iya, yawa]. 76 Zango Na: 2 Karatun Jimla Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana ta iya kwalliya]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [kwalliya]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Rubuta labarin a kan allo. Yau ma ana bikin sallah. Abba na yawon sallah. Nana ta iya kwalliya. Amina ma ta iya kwalliya. Sun sanya kayan yayi. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 77 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 4 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 7 da Na 8 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 25 a cikin littafin karatun a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [take, sauƙi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Yy, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 78 Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma. Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi. Tsari: Ɗalibi zai fito gaban aji, ya kwaikwayi ma’anar kalmar. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Tsaro irin tambayoyin da za a yi wa ɗalibai tun farko zai taimaka wa malamai wajen auna fahimtarsu. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 26 a Littafin Karatu a Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [ainun, damu]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [25] a cikin Littafin Karatu a Bayyane. Waiwaye Wane taimako ne jami’in/ar taimaka wa malamai ya/ta ba ka a cikin darussan da suka gabata? A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’an taimaka wa malamai? Ko kana da jami’in/ar da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/kike so jami’an su tattauna a lokacin taron malamai na gaba. 79 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Gaɓar Kalma A, i, o, u, e! A, i, o, u, e! Ba bi, bo, bu, be! Ba, bi, bo, bu, be! Ca, ci, co, cu, ce! Ca, ci, co, cu, ce! Da, di, do, du, deeeee!!! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [lada]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [langa, lauje, ludayi]. Jagoran Malamai - Aji 2 80 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 /O8X OXOXQEX OXQJXXOXODPEX $PLQDDOXQJXFLNLQODPEX .DUDWXQODEDUL /O/O/O 8X8X8 /XO8X/ $PLQDDOXQJXFLNLQODPEX 7DQDZDVDGDXOX *D1DQDGDOLWWDÀQNDUDWX 6DLVXND]DXQDWDUH Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Y, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 wani abu kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘leƙa’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [L l]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [L], sautinsa /l/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U u]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’ 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita matakin na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [L] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[L] na da sautin /l/ kamar a cikin kalmar leƙa.” Ka/ki kwatanta leƙa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [L, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 81 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [lu]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [lun, bu]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [lungu] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 9 da Na 10 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ulu, lambu]. 82 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Karatun Jimla Darasi Na 9 da Na 10 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 1. Rubuta jimlar a kan allo [Amina a lungu cikin lambu]. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cikin]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 5. Karanta jimlar kana aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 4. Rubuta labarin a kan allo. Amina a lungu cikin lambu. Tana wasa da ulu. Ga Nana da littafin karatu. Sai suka zauna tare. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 83 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Karatun Labari A Bayyane 1.Buɗa shafi na 27 a cikin littafin karatu a bayyane. Darasi Na 9 da Na 10 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [zaƙi, gudawa]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ll, Uu]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta harafin a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta harafin a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 84 Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma. Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi. Tsari: Ɗalibi/Ɗalibar da ya/ta gano kalmar da aka kwaikwaya shi zai/ita za ta kwaikwayi kalmar gaba. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Yi amfani da azancin tambaya cikin labari, don gano fahimtar ɗalibai wajen ba da amsa. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 28 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [likita, girma]. 3. Waiwaye Ka/ki tunafar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [27] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Me ka/kika fahimci na faruwa da ɗalibai a lokacin karatun labari a bayyane? Me ya kamata ka/ki yi don inganta karatun labari a bayyane? Bayan waiwaye me ya kamata ka/ki yi don inganta koyar da karatun labari a bayyane? 85 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gai da iyayen mu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin Amon sautin gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [ci]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ciki, ciniki, masallaci]. Jagoran Malamai - Aji 2 86 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 &F,L FLNLNLQ FLQQDNDFLNLQDELQFL &LQQDND\DFLML$PLQD .DUDWXQODEDUL &F&F& ,L,L, &L,F, 1DQDGD$PLQDFLNLQDML $PLQDQDFLQDELQFLDDML &LQQDND\DFLML$PLQD $PLQDWDMLFLZR Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [L, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 abinci kana/kina furta sautin ‘c’ ‘c’ ‘ ci’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [C c]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [C], sautinsa /c/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [C] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[C] na da sautin /c/ kamar a cikin kalmar ci.” Ka/ki ɗauki hannunka/ki kana/kina sakawa a baki alamar cin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [C, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 87 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ci]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ki, kin]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [cinnaka] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 11 da Na 12 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [cikin, abinci]. 88 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Karatun Jimla Darasi Na 11 da Na 12 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Cinnaka ya ciji Amina]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ciji]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Nana da Amina cikin aji. Amina na cin abinci a aji. Cinnaka ya ciji Amina. Amina ta ji ciwo. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da littafin Karatun ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 89 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 11 da Na 12 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 29 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kiyaye, haɗama]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Cc, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa akan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 90 Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Fahimta. Aiki: Manufa: Sake ba da labari. Don gano fahimtar ɗalibai. Tsari: Nemi ɗalibai su sake ba da labarin da ba su jima da saurara ba, ko kuma karantawa ba, kamar dai yadda ainihin marubucinsa ya zubo shi. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Koyar da sabbin kalmomi uku, don kafa tushen sani da fahimtar labari, tun kafin ɗalibai su saurari ‘Labarin Karatu a Bayyane. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 30 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [fari, matashi]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [29] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Me ya sa ka/kike ganin ɗaliban ka/ki sun taka rawar gani a wannan darasin? Ko ka/kikan yaba wa ɗaliban ka/ki lokacin da suka taka rawar gani? Ta wace hanya? Bayan waiwaye me ka/kike ganin za ka/ki iya yi don ƙara yaba wa ɗalibanka/ki? 91 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [hutu]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [huhu, hukuma, mahukumta]. Jagoran Malamai - Aji 2 92 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 +K8X KXODWX KXWXKXWDZDKXOD $OL\DFLUHKXODU$EED .DUDWXQODEDUL +K+K+ 8X8X8 +X8K+X /RNDFLQWDUD\D\L $EEDGD$OLVXQDKXWDZD $EED\DVDIDUDUKXOD $OL\DFLUHKXODU$EED $EED\DWXUHKDQQXQ$OL Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [C, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 hamma kana/kina furta sautin ‘h’ ‘h’ ‘hamma’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [H h]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [H], sautinsa /h/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U u]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’ 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [H] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[H] na da sautin /h/ kamar a cikin Kalmar hamma.” ka/ki kwatanta yin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [H, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 93 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [hu]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [la, tu]. Kalmomin da Za A Karanta Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta wannan kalmar [hutu] a kan allo. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 13 da Na 14 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [hutawa, hula]. 94 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Karatun Jimla Darasi Na 13 da Na 14 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Ali ya cire hular Abba]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cire]. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 4. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Rubuta labarin a kan allo. Lokacin tara ya yi. Abba da Ali suna hutawa. Abba ya sa farar hula. Ali ya cire hular Abba. Abba ya ture hannun Ali. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 95 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 13 da Na 14 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 31 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [rumfa, sha’awar]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Hh, Uu]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 96 Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Fahimta. Aiki: Mu Tambayi Juna. Manufa: Sanin labari ciki da waje. Tsari:Nemi ɗalibai su yi tambaya ɗaya, wadda amsarta na cikin labari. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara A tabbatar ɗalibai sun koyi rubuta baƙi daga hagu zuwa dama, sannan daga sama zuwa ƙasa, ta hanyar zagayen duba aiki a cikin aji. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 32 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [salaf, tabɗi]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [31] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Wace matsala ka/kike fuskanta wajen koyar da gano gaɓar kalma, kalmomin da za a karanta, da karatun jimla? Wane taimako ka/kike buƙata don inganta darasin ka/ki wajen koyar da ɗalibai? Bayan waiwaye me ka/kike ganin ya kamata masu kula da wannan shiri su yi don kawo canje-canje wajen gabatar da darasi? 97 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙa a kan allo. Waƙar Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Wanke hannu yara shi ne tsafta Tsafta Wanke baki yara shi ne tsafta Tsafta Wanka, wanki yara shi ne tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta Tsafta. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [shiru]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [shayi, shinkafa, shiririta]. Jagoran Malamai - Aji 2 98 Zango Na: 2 Mako Na: 8 6KVK,L Darasi Na 15 da Na 16 A Picture of Abba with a plate of rice and A’isha with cup of tea inside the classroom. Include children in the background making noise. VKLVKDUX VKD\LVKLUXWDVKL $PLQDWD]RGDVKD\L .DUDWXQODEDUL 6KVK6KVK ,L,L, 6KL,VK6K $PLQDWD]RGDVKD\L $EED\D]RGDVKLQNDID $EED\D]XEDUGDVKLQNDID <DUDVXQWDVKLVXQDVXUXWX Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [H, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 ka/ki a kan bakinka/ki kana/kina furta sautin ‘sh’ ‘sh’ ‘shiru’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Sh sh]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Sh], sautinsa /sh/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/ kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita matakin na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Sh] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Sh] na da sautin /sh/ kamar a cikin kalmar shiru.” Ka/ki aza yatsan 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Sh, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 99 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 8 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [shi]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [sha, ru]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [shayi] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 15 da Na 16 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [shiru, tashi]. 100 Zango Na: 2 Mako Na: 8 Karatun Jimla Darasi Na 15 da Na 16 Karatun Labari Minti-3 Minti-5 1. Rubuta jimlar a kan allo [Amina ta zo da shayi]. 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [zo]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Amina ta zo da shayi. Abba ya zo da shinkafa. Abba ya zubar da shinkafa. Yara sun tashi suna surutu. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 101 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 2 Mako Na: 8 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 15 da Na 16 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 33 a cikin littafin karatu a bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ɗanɗano, ƙauri]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Sh sh, Ii]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa, ko a bayan wani ɗalibi da suke tare. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 102 Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Fahimta. Aiki: Mu Tambayi Juna. Manufa: Sanin labari ciki da waje. Tsari:Nemi ɗalibai su yi tambaya ɗaya, wadda amsarta na cikin labari. Shawara Matashiya A Kan Darasi Na 2 Yi amfani da allon koyon rubutu na ɗalibai don ba da damar auna ƙwarewa a rubutu nan take. A lokacin da suka ɗaga allunansu don nuna yadda suke zana harafi, za a gani nan take. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 34 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [gutsuro, tsohuwa]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [33] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Me ka/kike ganin shi ne aikin jami’in/ar taimaka wa malamai? Me ka/kika ƙaru da shi tun fara wannan shiri zuwa yau? Bayan waiwaye waɗanne abubuwa ne ka/kike buƙatar ƙarin taimako a kan su? 103 Jagoran Malamai - Aji 2 Alamomi Aikin Malami/Malama: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi. Aikin Malami/Malama da Ɗalibai: A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa. Aikin Ɗalibai: A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu. Alamar Akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar ta akwati. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar akwati da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar ta da’ira. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar ta dala. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar dala da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar ta tauraro. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu zuwa ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Karatun Ɗalibai. Alamar Agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/ za ta ɗauka domin karantar da sashe. Jagoran Malamai - Aji 2 104 ZANGO NA 3 Mako 1 - 9 Darasi 1 - 18 105 Jagoran Malamai - Aji 2 Manufar Malamai da Ɗalibai Zango na 3 Jigo na 5 Kasuwa Manufar Malamai A ƙarshen wannan sashe, malamai su gano ɗaliban da suke samun matsala wajen karatu da rubutu sannan a shirya musu darussa na musamman a kan waɗannan ɓangarori: • • • • Mako na 1-4 Manufar Ɗalibai Fahimtar Ƙwayoyin Sauti: Bambance sautukan haruffa Karatu: Iya karanta gaɓar kalma da kalmomin da ake buƙata. Iya Karatu: Yin karatu cikin hanzari kamar yadda ya dace tare da kakkarya murya. Fahimta: Fahimtar labarin da aka karanta ta hanyar amsa tambayoyin da ke cikin labarin. A ƙarshen mako na 1-4 , ana son malamai su : Mako na 1: ‘F’ ‘f’ ‘A’ ‘a’ Mako na 2: ‘Ɗ’ ‘ɗ’ ‘A’ ‘a’ Mako na 3: ‘J’ ‘j’ ‘E’ ‘e’ Mako na 4: ‘Z’ ‘z’ ‘O’ ‘o’ San ƙwazon ɗalibai a wajen iya karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. San yi wa ɗalibai tambayo uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Shawara a kan Gwaji A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘F’ ‘Ɗ’ ‘J’ ‘Z’ da wasullan ‘A’ ‘E’ ‘O’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: • Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. • Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace Jagoran Malamai - Aji 2 Malamai su taimaka wa ɗalibai su duba irin gudummawar da suke bayarwa a gida sakamakon cinikin amfanin gona a garuruwansu. A ƙarshen mako na 1-4 , ana son ɗalibai su iya: San ƙwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karantasu da kuma ƙwazonsu su a wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • A wannan sashe, an gabatar da abubuwan da suka shafi muhimmancin saye da sayarwa a kasuwa. 106 Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • Mako na 1: ‘F’ ‘f’ ‘A’ ‘a’ Mako na 2: ‘Ɗ’ ‘ɗ’ ‘A’ ‘a’ Mako na 3: ‘J’ ‘j’ ‘E’ ‘e’ Mako na 4: ‘Z’ ‘z’ ‘O’ ‘o’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Ba da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Zango na 3 Jigo na 6 Aji Manufar Malamai A ƙarshen wannan sashe, malamai su gano ɗaliban da suke samun matsala wajen karatu da rubutu sannan a shirya musu darussa na musamman a kan waɗannan ɓangarori: • • • • Mako na 5-9 Manufar Ɗalibai Fahimtar Ƙwayoyin Sauti: Bambance sautukan haruffa Karatu: Iya karanta gaɓar kalma da kalmomin da ake buƙata. Iya Karatu: Yin karatu cikin hanzari kamar yadda ya dace tare da kakkarya murya. Fahimta: Fahimtar labarin da aka karanta ta hanyar amsa tambayoyin da ke cikin labarin. A ƙarshen mako na 5-9, ana son malamai su San ƙwazon da ɗalibai suke da shi wajen iya gane haruffan da aka koyar da su tare da iya karantasu da kuma ƙwazonsu su a wajen karanta gaɓoɓin kalma da karanta kalmomin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • • Mako na 5: ‘Ƙ’ ‘ƙ’ ‘U’ ‘u’ Mako na 6: ‘Ƙw’ ‘ƙw’ ‘Ai’ ‘ai’ Mako na 7: ‘Kw’ ‘kw’ ‘Ai’ ‘ai’ Mako na 8: ‘Gw’ ‘gw’ ‘Au’ ‘au’ Mako na 9: ‘Ɓ’ ‘ɓ’ ‘A’ ‘a’ San ƙwazon ɗalibai a wajen iya karanta labari da kuma fahimtarsa ta hanyar sauraren karatun ɗalibai. A wannan sashe, ɗalibai za su duba hanyoyi daban daban na kai da kawo zuwa kasuwa. Malamai su taimakawa ɗalibai danganta yanayin gidansu Nana – Nana na zama da kakanninta yayin da Abba ke zaune da iyayensu – menene ra’ayinsu a kan hakan. A ƙarshen mako na 5-9, ana son ɗalibai su iya: Gane haruffan da aka koyar da su tare da karanta su. Ana kuma son ɗaliban su iya karanta gaɓoɓin kalma da kalmonin da ke ɗauke da waɗannan haruffan: • • • • • Mako na 5: ‘Ƙ’ ‘ƙ’ ‘U’ ‘u’ Mako na 6: ‘Ƙw’ ‘ƙw’ ‘Ai’ ‘ai’ Mako na 7: ‘Kw’ ‘kw’ ‘Ai’ ‘ai’ Mako na 8: ‘Gw’ ‘gw’ ‘Au’ ‘au’ Mako na 9: ‘Ɓ’ ‘ɓ’ ‘A’ ‘a’ Karanta labari wanda ke ɗauke da kalmomin da aka karanta da kuma baƙin kalmomi. Hasashen abin da suke tsammani zai faru a cikin labarin da za a karanta musu. Ba da amsar tambayoyi uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar take cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Yi wa ɗalibai tambayo uku waɗanda suka ƙunshi tambaya wadda amsar ta ke cikin labarin da tambaya mai harshen damo da kuma tambayar jin ra’ayi Shawara a kan Gwaji A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘Ƙ’ ‘Ƙw ‘Kw’ ‘Gw’ ‘Ɓ’ da wasulan ‘U’ ‘Ai’ ‘Au’ ‘A’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon karatunsu a: 1. Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan da aka koyar. 2. Jimlolin da ke cikin labari da amsa tambayoyi daidai. Malamai su sake karantarwa a inda ya dace 107 A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya karanta haruffa da kalmomi da jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama. A ba ɗalibai aikin gida ko ayyuka don ƙarin ƙwarewa. Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Kafin Darasi Waƙa Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Motsa jiki Yara mu tafa, muna ta tafawa Mu tashi, muna ta tasawa Mu juya, muna ta juyawa Mu duƙa, muna ta duƙawa Mu zauna, muna ta zaunawa. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [fara]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [fari, fartanya, fatimatu]. Jagoran Malamai - Aji 2 108 Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 )I$D IDUDGD IDUDGDIDIDGDPD 6XQKDˆXGDIDGDZD .DUDWXQODEDUL )I)I $D$D$D )ID$ID $QDVD\DUGDIDUDDNDVXZD $PLQDWDVD\LIDUD 1DQDQDGDIDVKLQNDID =DVXNDLZDNDND 6XQKDŚXGDIDGDZD Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Sh, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [F, f]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [F], sautinsa /f/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [F] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[F] na da sautin /f/ kamar a cikin kalmar fere.” Ka/ki ɗaga yatsa ɗaya kana/kina mai kwatanta fere fensiri 109 kana/kina furta sautin ‘f’ ‘f’ ‘fere’. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [F, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Ka/ki nemi ɗalibai su faɗi sunayen haruffan. Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 1 Gano Gaɓar Kalma Darasi Na 1 da Na 2 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [fa]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ra, da]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [fara] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [dafa, fadama]. 110 Zango Na: 3 Karatun Jimla Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Sun haɗu da fadawa]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [haɗu]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. Ana sayar da fara a kasuwa. Aimina ta sayi fara. Nana na dafa shinkafa. Za su kai wa kaka. Sun haɗu da fadawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 111 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 1 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 1 da Na 2 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 36 a cikin littafin Karatu a Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gangara, rafi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin littafin Karatu a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ff, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kai/ke ma kake/kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 112 Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi:Tsarin Haruffan Harshe. Aiki: Ginin Gaɓoɓi. Manufa: Jaddada iya amfani da sauti. Tsari: Yi amfani da gaɓoɓin kalmar da aka koyar a cikin darasi (misali: ka, na). A rubuta su a jikin allo. Nemi ɗalibai su ƙirƙiro sabbin gaɓoɓi, ta hanyar canza haruffan farko (mislai: ta, ma). Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Yi amfani da duk damar da ka samu wajen ganin ɗalibai sun nuna iyawarsu ta hanyar sa su su rubuta haruffa ko kalmomin da aka koyar da su. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 37 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za’a koyar su ne [nutse, lura]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [36] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waɗanne abubuwa ka/kike yi don ƙawata aji da rubuce-rubuce? Me ya kamata ka/ki umurci ɗalibai su zo da su don ƙawata aji? Bayan waiwaye wace hanya za ka/ki mayar da ajin ka/ki abin sha’awa? 113 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar gaisuwa Idan muka tashi da safe Sai mu gai da iyayenmu x 2 Mamata ina kwana Gaisuwa ce da safe Ina wuni Babana Gaisuwa ce da rana Mamata sai da safe Gaisuwa ce da dare. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [ɗa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ɗaya, ƙafaɗa, mashinfiɗi]. Jagoran Malamai - Aji 2 114 Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 ŤŚ$D ŚDŚLJLU ŚDULIDŚLNDIDŚD $EED\DˆDXNLGDZD DNDIDˆDUVD .DUDWXQODEDUL ŤŚŤŚ /RNDFLQŚDULGDZDNDQQXQD /RNDFLQJLUEL\D\L .DNDGD$EEDVXQDJRQD .DNDGD$EEDVXQDJLUELQGDZD $EED\DŚDXNLGDZDDNDIDŚDUVD $D$D$D ŤD$ŚD˧ Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [F, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 ɗanɗana miya kana/kina furta sautin ‘ɗ’ ‘ɗ’ ‘ɗanɗano’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ɗ, ɗ]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ɗ], sautinsa /ɗ/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ɗ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ɗ] na da sautin /ɗ/ kamar a cikin kalmar ɗanɗano.” Ka/ki kwatanta 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ɗ, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 115 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 2 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ɗa]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ɗi, gir]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [ɗari] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 3 da Na 4 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [faɗi, kafaɗa]. 116 Zango Na: 3 Karatun Jimla Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Abba ya ɗauki dawa a kafaɗarsa]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ɗauki]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Lokacin ɗari dawa kan nuna. Lokacin girbi ya yi. Kaka da Abba suna gona. Kaka da Abba suna girbin dawa. Abba ya ɗauki dawa a kafaɗarsa. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 117 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 2 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 3 da Na 4 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 38 a cikin Littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gwada, daji]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ɗɗ, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 118 Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Tsarin Haruffan Harshe. Aiki: GininKalmomi. Manufa: Jaddada sanin haruffa a rubutu. Tsari: Ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen bin bahasin ɗaiɗaikun haruffa da kalmomin da aka gabatar musu a cikin darasi. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Katin ‘I’ ko ‘A’a’ - Yanki ’yan takardu ko kwalaye. Sai a rubuta ‘I’ a gaba, sannan ‘A’a’ a baya. Nemi ɗalibai su ɗaga katin wajen ba da amsar tambaya. Waiwaye 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 39 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [kunya, haƙuri] 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [38] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Me ka/kika fahimci na faruwa da ɗalibai a lokacin karatun labari a bayyane? Me ya kamata ka yi don inganta karatun labari a bayyane? Bayan waiwaye me ya kamata ka yi don inganta koyar da karatun labari a bayyane? 119 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [jera]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [jaki, gajere, gajiyayyu]. Jagoran Malamai - Aji 2 120 Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 -M(H MHMLMD GDMLMHNXMHUD =DLMHNDVXZDGDGDZD .DUDWXQODEDUL -M-M (H(H( -H(MH *D.DNDGDMDNLQVD <DMHUDGDZDDED\DQMDNL =DLMHNDVXZDGDGDZD -DNL\DELWDGDMLDJXMH .DND\DQDELQMDNLDED\D Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ɗ, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 kalmar ji.” Ka/ki riƙe kunne kana/ kina furta sautin ‘j’ ‘j’ ‘ji’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [J j]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [J], sautinsa /j/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [E, e] 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [E] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [E] na da sautin /e/ kamar a cikin kalmar eeh.” Ka/ki riƙa sunkuyar da kai sama da ƙasa alamar aminicewa kana/kina furta sautin ‘e’ ‘e’ ‘eeh’. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [J] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[J] na da sautin /j/ kamar a cikin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [J, E], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 121 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 3 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [je]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ji, ja]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [daji] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 5 da Na 6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [je, kujera]. 122 Zango Na: 3 Karatun Jimla Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Zai je kasuwa da dawa]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [zai]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Ga Kaka da jakinsa. Ya jera dawa a bayan jaki. Zai je kasuwa da dawa. Jaki ya bi ta daji a guje. Kaka yana bin jaki a baya. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jumlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 123 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 3 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 5 da Na 6 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 40 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙirga, tunani]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Jj, Ee]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 124 Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Iya Karatu. Aiki: Maimaita Karatu. Manufa: Haɓaka ƙwarewar ɗalibai ta hanyar yawan ganin kalmomi da kuma aiki da su. Tsari: Faɗa wa ɗalibai cewa, suna karanta labarin ne don su ƙara ƙwarewa wajen iya karatu, da sanin kalmomi, da muhallinsu, da kuma karanta kalma ba da tangarɗa ba. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Ana son malamai su mammanna hotuna ko kalmomi, ko tsarin baƙaƙe, ko wata waƙa, ko kuma aikin ɗalibai a wurare daban-daban a cikin aji. Waiwaye 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 41 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [lura, hira]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [40] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Me ya sa ka/kike ganin ɗalibanka/ki sun taka rawar gani a wannan darasin? Ko ka/kikan yaba wa ɗalibanka/ki lokacin da suka taka rawar gani? Ta wace hanya? Bayan waiwaye me ka/kike ganin za ka iya yi don ƙara yaba wa ɗalibanka? 125 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Gaɓar Kalma A, i, o, u, e! A, i, o, u, e! Ba bi, bo, bu, be! Ba, bi, bo, bu, be! Ca, ci, co, cu, ce! Ca, ci, co, cu, ce! Da, di, do, du, deeeee!!! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [zo]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [zane, zakara, zabarmawa]. Jagoran Malamai - Aji 2 126 Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 =]2R ]R]DQH =RPR=DQH=DNDUD $JLGDQ.DNDDNZDL GDEEREL .DUDWXQODEDUL =]=] 2R2R2 =R2]R $JLGDQ.DNDDNZDLGDEEREL 1DQDQDGD]RPRGD]DNDUD =RPRQDWRQRDJLQGLQELVKL\D =DNDUDQDFLQGDZD 1DQDWDNRUL]DNDUDGDJXGX Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [J, E]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Minti-6 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Z z]. 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [O o]. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Z], sautinsa /z/.” 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [O] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [O] na da sautin /o/ kamar a cikin kalmar oho.” Ka/ki riƙa buɗe hannayenka/ki kana/kina ɗaga kafaɗa nuna alamar rashin damuwa kana/kina furta sautin ‘o’ ‘o’ ‘oho’. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Z] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Z] na da sautin /z/ kamar a cikin kalmar zane.” Ka/ki kwatanta yin zane. kana/kina furta sautin ‘z’ ‘z’ ‘zane’. 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Z, O], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 127 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 4 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [zo]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [za, ne]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [zomo] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 7 da Na 8 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [zane, zakara]. 128 Zango Na: 3 Karatun Jimla Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [A gidan Kaka akwai dabbobi]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [akwai]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. A gidan Kaka akwai dabbobi. Nana na da zomo da zakara. Zomo na tono a gindin bishiya. Zakara na cin dawa. Nana ta kori zakara da gudu. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 129 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 4 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 7 da Na 8 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 42 a cikin Littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙanwa, lambu]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Zz, Oo]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-5 130 Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Iya Karatu. Aiki: Maimaita Karatu. Manufa: Haɓaka ƙwarewar ɗalibai ta hanyar yawan ganin kalmomi da kuma aiki da su. Tsari: Sa ɗalibai su maimata karatu sau da dama, sannan a auna fahimtarsu. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Nemi ɗalibai su gwada rubuta kalmomin da suka ga an mammanna a cikin aji, bayan sun gama ayyukan da aka sa su sa. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 43 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [hira, wasa]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [42] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Me ya fi faranta maka/miki rai a wannan darasin na yau? Wane ɓangare ne na darasin yau bai yi maka/miki daɗi ba? Bayan waiwaye waɗanne ɓangarori ne ka/kika samu nasara a kan su cikin waɗanda ka/kika taɓa samun matsala da su? 131 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Ƙirge ɗaya mafarin ƙirge Biyu idanun dabba Uku duwatsun murhu Huɗu ƙafafun tebur Biyar na yatsun hannu 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [ƙura]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ƙurji, ƙuruciya, baƙunci]. Jagoran Malamai - Aji 2 132 Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Ǔ ǎ 8X ǎXJXUD ǎXUDWXǎDǎXVD 0RWDU%DEDWD\L ֜XUDVRVDL .DUDWXQODEDUL ǓǎǓǎǓ 8X8X8 ǓXǎ8ǓX %DEDGDPDPDDPRWD 6XQDGDZRZDGDJDNDVXZD %DED\DQDWXǎDPRWD 0RWDU%DEDWD\LǎXUDVRVDL ǓXVDWDIDVDWD\DUPRWDU%DED Sunayen Haruffa da Sautukansu 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Z, O]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ƙ ƙ]. Minti-6 kwatanta yin ƙirge kana/kina furta sautin ‘ƙ’ ‘ƙ’ ‘ƙirge’. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ƙ], sautinsa /ƙ/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U, u]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’ 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ƙ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ƙ] na da sautin /ƙ/ kamar a cikin kalmar ƙirge.” Ka/ki ɗaga hannunka/ki sama kana/kina 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ƙ, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 133 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 5 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ƙu]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [gu, ra]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [ƙura] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 9 da Na 10 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [tuƙa, ƙusa]. 134 Zango Na: 3 Karatun Jimla Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [motar Baba ta yi ƙura sosai]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [sosai]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa. 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. Baba da mama a mota. Suna dawowa daga kasuwa. Baba yana tuƙa mota. Motar Baba ta yi ƙura sosai. ƙusa ta fasa tayar motar Baba. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 135 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 5 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 9 da Na 10 Minti-5 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 44 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙiba, attarugu]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ƙƙ, Uu]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 136 Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Iya Karatu. Aiki: Karatun Tare. Manufa: Yi amfani da maimaita karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su ƙwarin gwiwa. Tsari: Haɗa ɗalibai, sannan ka tsamo labarin da za su yi aiki a kai. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Samar da babbar takarda da ke ɗauke da baƙin kalmomi da ɗalibai za su ci karo da su a littattafansu. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 45 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [bayani, tsumbure]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [44] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Wane cigaba kake/kike ganin ɗaliban ka/ki suke samu a cikin darussan ka/ki? Ko akwai ɓangarorin darussanka/ki da ba ka/ki ji daɗin fahimtar ɗaliban ka/ki a kan su ba? Bayan waiwaye waɗanne ɓangarori ne ɗalibanka/ki suka fi samun nasara a wannan shekara? 137 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙar a kan allo. Waƙar Haruffa a, b, c, d, e, f, g, h! i, j, k, l, m, n, o, r! s, t, u, w, y, z! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. An taso daga makaranta ‘Ya’yan kaji na wasa Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba! 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [ƙwai]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ƙwarewa, ƙwarai, maƙwabtaka]. Jagoran Malamai - Aji 2 138 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 ǓZǎZ$LDL ǎZDLǎZDDL ǎZDLǎZDU\DǎZDUDL .DNDWDˆDXNL ֜ZDLD֜ZDU\D .DUDWXQODEDUL 1DQDQDWDUDǎZDLDǎZDU\D .DNDGDPDǎZDEWDQWD]DVXNDVXZD .DNDWDŚDXNLǎZDLDǎZDU\D 0DǎZDEFL\DUWDWDŚDXNRǎZDǎZDǎZD ǓZDU\DU.DNDWDQDGDN\DXǎZDUDL ǓZǎZǓZǎZ $L DL$LDL$L ǓZ֜Z$LDL Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 hammata kana/kina karkaɗawa kana/kina furta sautin ‘ƙw’ ‘ƙw’ ‘ƙwaƙwaƙwa’. 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ƙ, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ƙw, ƙw]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ƙw], sautisa /ƙw/.” 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Ai, ai]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ai] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Ai] na da sautin /ai/ kamar a cikin kalmar aiki.” Ka/ki kwatanta yin wani aiki kana/ kina furta sautin ‘ai’ ‘ai’ ‘aiki’. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ƙw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ƙw] na da sautin /ƙw/ kamar a cikin kalmar ƙwaƙwa.” Ka/ ki lanƙwasa hannunka/ki zuwa 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ƙw, Ai], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 139 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ƙwai]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ƙwa, ai]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [ƙwai] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 11 da Na 12 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ƙwarya, ƙwarai]. 140 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Karatun Jimla Darasi Na 11 da Na 12 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Kaka ta ɗauki ƙwai a ƙwarya]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ɗauki]. 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4.Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa 6.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Karanta jimlar tare da ɗalibai. Nana na tara ƙwai a ƙwarya. Kaka da maƙwabtanta za su kasuwa. Kaka ta ɗauki ƙwai a ƙwarya. Maƙwabciyarta ta ɗauko ƙwaƙwaƙwa. ƙwaryar Kaka tana da kyau ƙwarai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 141 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 11 da Na 12 Minti-5 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin. 1.Buɗa shafi na 46 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gane, hali]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ƙw ƙw, AI ai]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 142 Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Iya Karatu. Aiki: Karatun Tare. Manufa: Yi amfani da maimaita karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su ƙwarin gwiwa. Tsari: Nemi ɗalibi ɗaya ya karanta labarin sau uku, shi kuma ɗaya ɗalibin ya yi bayani a kan abu guda da aka karanta sosai, da kuma abu ɗaya wanda za a gyara a gaba. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Manna sabuwar kalma a kowace rana, kuma a nemi ɗalibai su gano/faɗi ma’anar kalmar. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 47 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [attajiri, kuka]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [46] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Waɗanne irin abubuwa ne ka/kika samu gudumawa a kan su daga jami’an taimaka wa malamai a wannan shekara? Waɗanne ɓangarorin darasi ne shugaban makaranta ya taimaka maka/ki a kan su a wannan shekara? Bayan waiwaye me ka inganta daga cikin taimakon horon da ka samu daga jami’an taimaka wa malamai da kuma shugaban makaranta? 143 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta wannan waƙar a kan allo. Waƙar Ƙirge Ɗaya mafarin ƙirge Biyu idanun dabba Uku duwatsun murhu Huɗu ƙafafun tebur Biyar na yatsun hannu. 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [akwai]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [kwaikwayo, bakwai, ƙwabbai]. Jagoran Malamai - Aji 2 144 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 .ZNZ$LDL NZDLNZD\R NZDNZDNZDLNZD\R DNZDL 1DQDQDNZDLNZD\RQ NZDOOL\DU0DPD .DUDWXQODEDUL 1DQDWDMHJDULQ5LQJLPL 0DPDQDNZDOOL\DDFLNLQŚDNL 1DQDQDNZDLNZD\RQNZDOOL\DU0DPD 6XQ\LNZDOOL\D]DVXMHNDVXZD =DVXVD\RNDMLJXGDEDNZDL 6XQJDNZDQRFLNHGDNZDNZD .ZNZ.ZNZ $L DL$L DL $L .ZNZDL Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 kwatanta yin kwalliya kana/kina furta sautin ‘kw’ ‘kw’ ‘kwalliya’. 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ƙw, Ai]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Kw, kw]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Kw], sautinsa /kw/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Ai, ai]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ai] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Ai] na da sautin /ai/ kamar a cikin kalmar aiki.” Ka/ki kwatanta yin wani aiki kana/ kina furta sautin ‘ai’ ‘ai’ ‘aiki’. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [kw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Kw] na da sautin /kw/ kamar a cikin kalmar kwalliya.” Ka/ki 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Kw, Ai], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 145 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Gano Gaɓar Kalma Darasi Na 13 da Na 14 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [kwai]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [kwa, yo]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [kwakwa] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Minti-6 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [kwaikwayo, akwai]. 146 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Karatun Jimla Darasi Na 13 da Na 14 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na kwaikwayon kwalliyar Mama] Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin ta su fahimta. 4. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. Nana ta je garin Ringimi. Mama na kwalliya a cikin ɗaki. Nana na kwaikwayon kwalliyar Mama. Sun yi kwalliya za su je kasuwa. Za su sayo kaji guda bakwai. Sun ga kwano cike da kwakwa. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 147 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 13 da Na 14 Minti-5 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 48 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [makirci, rarraba]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Kw kw, AI ai]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 148 Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Koyon Sabuwar Kalma. Manufa: Ba ɗalibai dama su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen makaranta. Tsari: Keɓe ‘yan mintina a mako domin samun jin bayanin yadda ɗalibai suka tsinci kalma, da kuma ma’anarta. Nemi ɗalibai su fito su rubuta kalmominsu a jikin allo. Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. Manna wannan tsarin ba da labarai, wanda zai taimaka wa ɗalibai wajen gina labari, kamar haka: 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 49 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [rani, shanuwa]. Taken Labari Farkon Labari Tsakiyar Labari Waiwaye 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [48] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Ƙarshen Labari A farkon shekaran nan waɗanne matsaloli ne ka/kika samu wajen tsarin darasin ka/ki? Me kake/kike ganin ya sa kake/kike cigaba da samun waɗannan matsaloli? Bayan waiwaye waɗanne shawarwari ne za ka/ki iya ba malamai a wajen taron malamai? 149 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Gaɓar Kalma A, i, o, u, e! A, i, o, u, e! Ba bi, bo, bu, be! Ba, bi, bo, bu, be! Ca, ci, co, cu, ce! Ca, ci, co, cu, ce! Da, di, do, du, deeeee!!! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [gwauro]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [gwaza, gwaiba, gwauruwa]. Jagoran Malamai - Aji 2 150 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 *ZJZ$XDX JZDXJZDL]D JZDXURJZD]DJZDLED <DKDˆXGDJZDXUR DKDQ\D * Z JZ * Z JZ $XDX$XDX *ZDXJZ$X .DUDWXQODEDUL .DNDGDMDNLQVD]DLMHNDVXZD <DQDŚDXNHGDEXKXQJZD]D <DKDŚXGDJZDXURDKDQ\D .DND\DGDZRGDJDNDVXZD <DVD\RZD1DQDNZDQGRQJZDLED Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 gwalo kana/kina furta sautin ‘gw’ ‘gw’ ‘gwalo’. 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Kw, Ai]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Gw gw]. 8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Gw], sautinsa /gw/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Au au]. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Au] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Au] na da sautin /au/ kamar a cikin kalmar auna.” Ka/ki kwatanta auna hatsi kana/kina furta sautin ‘au’ ‘au’ ‘auna’. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Gw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Gw] na da sautin /gw/ kamar a cikin kalmar gwalo.” Ka/ki riƙa yin 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Gw, Au], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 151 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [gwau]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [gwai, za]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [gwauro] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-dabann. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 15 da Na 16 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [gwaza, gwaiba]. 152 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Karatun Jimla Darasi Na 15 da Na 16 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Ya haɗu da gwauro a hanya]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 4. Rubuta labarin a kan allo. 5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. Kaka da jakinsa zai je kasuwa. Yana ɗauke da buhun gwaza. Ya haɗu da gwauro a hanya. Kaka ya dawo daga kasuwa. Ya sayo wa Nana kwandon gwaiba. 6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 153 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 15 da Na 16 Minti-5 4.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 50 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [tumu, damina]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 6.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun Labarai a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [GW gw, AU au]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 154 Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi: Kalmomi. Aiki: Koyon Sabuwar Kalma. Manufa: Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen makaranta. Tsari: Samar da waje, ko allon manna sabbin kalmomi. Matashiya A kan Darasi Na 2 Shawara Ana son malamai su mammanna hotuna da sabbin kalmomi, ko tsarin baƙaƙe, ko wata waƙa, ko kuma aikin ɗalibai a wurare daban-daban a cikin aji. Waiwaye 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 51 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [face, gudummawa]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [50] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. A farkon wannan shiri waɗanne ɓangarori ne ka/kika samu matsala da su a cikin darasin ka/ki? Daga cikin waɗannan matsalolin da ka/kika rubuta a sama, yanzu waɗanne ka/kika samu cigaba a kan su? Bayan waiwaye wace shawara za ka/ki iya ba sabon malami/ma a wannan shirin? 155 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18 Waƙa Kafin Darasi Minti-3 1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar. 1. Rubuta waƙar a kan allo. Waƙar Gaɓar Kalma A, i, o, u, e! A, i, o, u, e! Ba bi, bo, bu, be! Ba, bi, bo, bu, be! Ca, ci, co, cu, ce! Ca, ci, co, cu, ce! Da, di, do, du, deeeee!!! 2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo. 3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa. 5.Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin. Amon Sautin Gaɓa Minti 2 1. Furta wannan kalma [ɓalle]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu. 2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa. 3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu. 4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke. 5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ɓera, ɓangare, ɓanɓarowa]. Jagoran Malamai - Aji 2 156 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18 ņł$D łDłXOłH łDWDłXOORZDWDłDU\D 7DȶDU\DU.DNDWDȶDWD .DUDWXQODEDUL ņłņłņ $D$D$ ņDł$ņD 7DłDU\DU.DNDWDłDWD 1DQDGD$PLQDVXQÀWDQHPDQWDłDU\D 1DQDWDJDQRWDłDU\DDKDQ\DUNDVXZD $PPDWDłDU\DUWDłDFLDJHIHŚD\D .DNDWD\LPXUQDUJDQLQWDłDU\DUWD Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6 kana/kina ɓare wani abu kana/kina furta sautin ‘ɓ’ ‘ɓ’ ‘ɓare’. 1. A tuna wa ɗalibai haruffan da suka gabata [Gw, Au]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 7.Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama. 2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ɓ ɓ]. 8. Maimaita mataki na batkwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban. 3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ɓ], sautinsa /ɓ/.” 9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a]. 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai dabandaban. 10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’ 11. Maimaita mataki na shida da na bakwai (6-7). 6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ɓ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ɓ] na da sautin /ɓ/ kamar a cikin kalmar ɓare.” Ka/ki riƙa yin kamar 12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ɓ, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. 157 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Gano Gaɓar Kalma Minti-6 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (23) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ɓa]. 2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/ kina furta sautinta da sauri. 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ɓul, ɓe]. Kalmomin da Za A Karanta 1. Rubuta wannan kalmar [ɓata] a kan allo. Minti-5 4.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali. 5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri. Jagoran Malamai - Aji 2 Darasi Na 17 da Na 18 6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ɓullowa, taɓarya]. 158 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Karatun Jimla Darasi Na 17 da Na 18 Karatun Labari Minti-3 1. Rubuta jimlar a kan allo [Taɓaryar Kaka ta ɓata ]. Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu. 2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa 2.Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa. 3.Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Karatun Ɗalibai. 3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta. 4. Rubuta labarin a kan allo. 4. Karanta jimlar tare da ɗalibai. 5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai dabandaban. Taɓaryar Kaka ta ɓata Nana da Amina sun fita neman taɓarya. Nana ta gano taɓarya a hanyar kasuwa. Amma taɓaryar ta ɓaci a gefe ɗaya. Kaka tayi murnar ganin taɓaryarta. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma. 6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Karatun Ɗalibai. 7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban. 159 Jagoran Malamai - Aji 2 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Karatun Labari A Bayyane Darasi Na 17 da Na 18 Minti-5 3.Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin. 1.Buɗa shafi na 52 a cikin littafin Karatu A Bayyane. 2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau. 4. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai. 2. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [sharri, maƙoshi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna. 5.Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu. 6. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun a Bayyane. Rubuta Haruffa Minti-5 1.Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ɓɓ, Aa]. 2.Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/ kike tisawa a kan allo. 3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa. 4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu. 5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa. Jagoran Malamai - Aji 2 160 Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18 Aikin Gida 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai. 2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu. Ayyukan ƙara ƙwarewa Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban. Reshen Darasi:Tsarin Haruffan Harshe. Aiki: Ginin Kalmomi. Manufa: Jaddada iya amfani da sauti. Tsari: Yi amfani da gaɓoɓin kalmar da aka koyar cikin darasi (misali: ka, na). A rubuta su a kan allo. Nemi ɗalibai su ƙirƙiro sabbin gaɓoɓi, ta hanyar canza baƙaƙen farko (mislai: ta, ma). Matashiya A Kan Darasi Na 2 Shawara Ba su dama su furta kalmomi, tare da jinsu a cikin waƙa yana haɓaka fahimtarsu ta sauraro da gina kalmomi. 1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata. 2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 53 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [gallaza, fatake]. 3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [52] a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Waiwaye Na fahimci yawancin ɗalibai sun fi son: Na fi jin daɗin koyar da waɗannan : A kundin na ina iya koyar da waɗannan a sauran darussana na yau: 161 Jagoran Malamai - Aji 2 Rataye Kalmomin Aikin Koyar Da Karatu Tsarin Haruffan Hausa Tsarin haruffan Hausa na nunin yadda jadawalin harruffan Hausa suke tare da yadda ake haɗa su don tayar da gabar kalma, waɗanda da su ne ake tayar da kalma. Daga ƙarshe a haɗa kalmomin don tada jimla Gwaji Gwaji hanya ce ta lura da kuma auna fahimtar ɗalibai. Fahimta Fahimta ita ce fitar da ma’ana daga abin da aka rubuta ko aka koyar. Bayani dalla-dalla Hanya ce ta koyarwa, inda ake fitar da abin da batu ya ƙunsa dalladalla don ƙarin fahimta. Iya Karatu Iya karatu na nufin karanta rubutu da sauri tare da furta kalmomi daidai. Tsarin Darasi Hanyar gabatar da darasi da ke ƙunshe da manufar aiki da kuma lokacin kammala shi. Fahimtar Ƙwayoyin Sauti Fahimtar ƙwayoyin sauti na nufin ƙwarewa wajen saurare, da rarrabewa da kuma sarrafa ɗaiɗaikun sautuka a cikin magana. Sanannun Kalmomi Kalmomi ne sanannu da suka bijiro sakamakon gabatar da wani sabon darasi. Tsarin Koyarwa Darasin da aka gina a kan aikin da ya gabata, mai fitacciyar manufar koyar da wani aiki ga ɗalibai. Baƙin kalmomi Kalmomi su ne kalmomin da dole ɗalibai su san su kafin su fahimci abin da su ka gani a rubuce ko su ka ji a labari. Matakan Bunƙasa Koyon Karatu Rarrafe Tashi Tattakawa Faɗi-tashi Tafiya Sassarfa Mataki Ɗan Koyo Rarrafe Yaro yana jin harshen uwa, amma sai da hotuna yake iya ganewa; zai nuna kamar ya iya karatu; yana jin tushen kalmomi. Jagoran Malamai - Aji 2 162 Harafi Motsi Bayanin Motsi N Noma A Ah! K Kama M Moow S Saƙa T Tafi I Ido R Rawa D Daka Ts Tsalle B Boom W Wanka G Y Gudu Yanka L Leƙa U Ungo C Ci H Sh Hamma Shiru F Fere Ɗ Ɗanɗano Malami/Malama ya/ta nuna yadda ake noma da fartanya, yana/tana furta sautin ‘n’ ‘n’ ‘noma’ Malami/Malama ya/ta ɗaga hannunsa/ta sama cikin mamaki yana/ tana furta sautin ah! ah! Malami/Malama ya/ta ɗaga hannunsa/ta na hagu, ya/ta kama na dama, yana/tana furta sautin ‘k’ ‘k’ ‘kama’ Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗagawa da miƙa wuyansa/ta gaba, yana/ tana kwaikwayon kukan saniya wajen furta sautin ‘m’ ‘m’ ‘mmmooow’ Malami/Malama zai/za ta yi kamar yana/tana saƙa da hannuwansa/ta, yayin da yake/take furta sautin ‘s’ ‘s’ ‘saƙa’ Malami/Malama ya/ta dinga tafa hanuwansa/ta yana/tana furta sautin ‘t’ ‘t’ ‘tafi’ Malami/Malama ya/ta nuni idonsa/ta da yatsa, yana/tana furta sautin ‘I’ ‘I’ ‘Ido’ Malami/Malama ya/ta kwatanta yin rawa yana/tana furta sautin ‘r’ ‘r’ ‘rawa’ Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗaga hannuwansa/ta sama yana/tana sako su kamar mai daka, yayin da yake/take furta sautin ‘d’ ‘d’ ‘daka’ Malami/Malama zai/za ta daka tsalle, kuma yana/tana furta sautin ‘ts’ ‘ts’ ‘tsalle’ Malami/Malama ya/ta nuna kamar yana/tana saman babur yana/tana murɗa hannun babur ɗin yana/tana furta sautin ‘b’ ‘b’ ‘boom- boom’ Malami/Malama ya/ta kwaikwayi cuɗar jiki, kuma yana/tana furta sautin ‘w’ ‘w’ ‘wanka’ Malami ya rinƙa sassarfa a cikin aji yana furta sautin ‘g’ ‘g’ ‘gudu’ Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana yanka da hannu ɗaya, kuma yana/tana furta sautin ‘y’ ‘y’ ‘yanka’ Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana leƙen wani abu, kuma yana/ tana furta sautin ‘l’ ‘l’ ‘leƙa’ Malami/Malama ya/ta miƙa hannunsa/ta zuwa wani ɗalibi/ɗaliba, kamar zai/za ta ba shi/ta wani abu, yana/tana furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo’ Malami/Malama zai/za ta yi kamar yana/tana cin abinci da hannu, kuma yana/tana furta sautin ‘c’ ‘c’ ‘ci’ Malami/Malama ya/ta yi hamma, yana/tana furta sautin ‘h’ h’ ‘hamma’ Malami/Malama ya/ta aza yatsansa/ta a kan bakinsa/ta yana/tana furta sautin ‘sh’ ‘sh’ ‘shiru’ Malami/Malama ya/ta ɗaga yatsansa/ta ya/ta kwaikwayi fere fensiri, kuma yana/tana furta sautin ‘f’ ‘f’ ‘fere’ Malami/Malama ya/ta kwaikwayi ɗanɗanar miya, yana/tana furta sautin ‘ɗ’ ‘ɗ’ ‘ɗanɗano’. 163 Jagoran Malamai - Aji 2 Harafi Motsi Bayanin Motsi J Ji E Eeh! Z Zane O Oho! Ƙ Ƙirga Ƙw Ƙwaƙwaƙwa Ai Aiki Kw Kwalliya Gw Gwalo Au Auna Ɓ Ɓare Malami/Malama ya/ta riƙe kunnensa/ta kamar yana/tana gargaɗi, kuma yana/tana furta sautin ‘j’ ‘j’ ‘ji’ Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗaga kai yana/tana noƙe shi don nuna amincewa, kuma yana/tana furta sautin ‘e’ ‘e’ ‘eeh!’ Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana zane, kuma yana/tana furta sautin ‘z’ ‘z’ ‘zane’ Malami/Malama ya/ta buɗe hannayensa/ta, tare da ɗaga kafaɗunsa/ta, yana/tana yin ko oho, kuma yana/tana furta sautin ‘o’, ‘o’, ‘oho’ Malami/Malama ya/ta nuna yana/tana ƙirga da yatsunsa/ta, kuma yana/tana furta sautin ‘ƙ’ ‘ƙ’ ‘ƙirga’ Malami/Malama ya/ta kwaikwayi tafiyar agwagwa, yana/tana ɗaga hannayensa/ta yana/tana sakinsu, kuma yana/tana furta sautin ‘ƙw’ ‘ƙw’ ‘ƙwaƙwaƙwa’ Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana wani aikin da ke son natsuwa, kuma yana/tana furta sautin ‘ai’, ‘ai’, ‘aiki’ Malami/Malama ya/ta kwatanta shafa hoda, kuma yana/tana furta sautin ‘kw’ ‘kw’ ‘kwalliya’ Malami/Malama ya/ta zuro harshensa/ta yana/tana gwalo, kuma yana/ tana furta sautin ‘gw’ ‘gw’ ‘gwalo’ Malami/Malama ya/ta kwatanta auna hatsi da hannunsa/ta, kuma yana/tana furta sautin ‘au’, ‘au’, ‘auna’ Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana ɓare wani abu, yana/tana furta sautin ‘ɓ’ ‘ɓ’ ‘ɓare’. Jagoran Malamai - Aji 2 172 Zango Na: 2 Jagoran Malamai - Aji 2 Mako Na: 5 184 Darasi Na 9 da Na 10