Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)

Transcription

Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
Juya waken soya da masara a gona
(kowace shekara)
Tare da hadin gwiwar
IAR, SG2000, ADPs, NEARLS, da DGDC–Belgium
Juya waken soya da masara a gona
(kowace shekara)
Shekara ta 1: Shuka waken soya
Shekara ta 2: Shuka masara a gona
Faidoji:
• Waken soya na kara sinadarin nitrogen a gona
• Zaka iya samun lafiyayyar masara a gona da ka noma waken
soya bara, ba tare da kashe kudi masu yawa ba wajen sayen
takin uriya.
• Shuka waken soya a wuri na kashe kaifin matsalar wuta-wuta.
• Noma waken soya da masara na samar da dinbin abinci na
mutane da kuma dabbobi. Bugu da kari kuma an yawaita
nau’in amfanin gona.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
1
Shekarar ta 1: Shuka
waken soya
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
3
1 Nemi ingantaccen
irin waken soya daga
kanfanin iri na kwarai.
Kana bukatar kilo 40
zuwa 50 na iri a kowace
hekta.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
4
2 Yi amfani da takin
zamani. Watsa buhu
shidda na takin supa a
kowace hekta kafin ayi
huda.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
5
3 Kayi hudar hannu
ko ta shanu ka tantan.
Ka ja kunyoyi masu
nisan sentimita 50
tsakanin su da juna.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
6
4 Da zarar an sami
isasshiyar lema, sai
ka yi layi mai zurfin
sentimita 1–2 ka saka
kwaya daya-daya kacal
a tazarar sentimita 5.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
7
5 A tsare tsuntsaye
har sati biyu daga ranar
shuka.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
8
6 Ka nemi shawarar
malamin gona wajen
kawar da haki da
maganin da ya dace in
ba fartanya zaka sa ba.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
9
7
Ka nemi
shawarar malamin
gona wajen amfani
da maganin feshi
da zarar kwari sun
bayyana a gona.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
10
8 Da zarar ganyayen
sun fara ja to waken
soya ya kosa. Ka sa
lauje wajen yanko shi
tun daga tushe. Kashe
din ka da a tuge shi da
hannu!
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
11
sh
e.
ca
an
an
ay
ab
on
ag
ar
ug
ra
za
ba
A
r
Kara ma gona taki
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
12
ga
au
ir i
ob ak
bb i t
da am
ba ka s
Ka on
d
CASA
9 Idan ka case waken
soyar ka sai ka baza
raugar a gona ko kuma
ka ciyarda dabbobi a
gona don kara ma gona
taki.
Shekara ta 2: Shuka
masara a gona
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
13
1 Ka nemi
ingantaccen irin
masara daga
kamfanin iri na
kwarai.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
14
2 A fasa tsaffin
kunyoyi don yin sabbin
a nisa sentimita 75
tsakanin kowace kunya.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
15
3 A yi shuka da zarar
ruwan sama ta wadata.
Yi ramu masu zurfin
sentimita 25 a kan
kunyoyi. Ka shuka
kwaya daya kacal a
kowane rami.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
16
4 Nemi shawarar
malamin gona wajen
amfani da maganin
kashe ciyawa kafin
tsirowar masara ko
kuma ka sa fartanya in
masara ta tsiro.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
17
5a Ka sanya buhu 3
na takin kamfa (NPK
15-15-15) sati daya da
yin shuka. Ka tona rami
mai nisan sentimita 5
daga jikin shuka ka zuba
cikin marfin kwalbar
lemu ka da kasa ta rufe.
5b Da zarar masara ta
kai tsawon gwiwa, ka
zuba buhu 3 na uriya
shima a rami mai nisan
sentimita 5 daga gindin
shukar ka zuba cikin
marfin kwalba lemu
kabi da kasa a rufe.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
18
6 Ka lankwasa
gayayyakin masara don
ta yi saurin bushewa da
kuma rage asara.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
19
7 Ka rika bare goyon
masara tun a lokacin
girbi.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
20
8 Ka baza masara ta
bushe sarai kafin ajiya.
Juya waken soya da masara a gona (kowace shekara)
21

Similar documents