Trauma Relief Flier 2 [hausa]

Transcription

Trauma Relief Flier 2 [hausa]
a l auMhua
h am
mm
m ee
d d
F o uFnod aut ino d
n ation
M u r t aMl uar tM
Matakan juriya bayan
jirkitar hankali sanadiyyar
Hadari ko Annoba
This leaflet is based on material produced by
the Royal College of Psychiatrists
(www.rcpsych.ac.uk/info). © 2014
The Royal College of Psychiatrists.
Reproduced by permission.
GABATARWA
Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya,
afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu
abubuwa ne da kan jefa mu cikin bakin
ciki, firgici da alhini. Haka kuma, suna da
tasiri mutuka wajen haifar da gagarimar
dimuwa mai karfin gaske, wanda yakan
raguwa da lokaci ba tare da ziyartar wasu
kwararrun taimako ba.
WANNAN TAKARDAR NA IYA
TAIMAKA MAKA IDAN:
•
Ka tsinci kanka cikin halin rudewa,
sakamakon wani hadari ko annoba, kuma
kana bukatar fahimtar halin da kake?
•
Ko ka san wani wanda yake cikin
halin dimuwa, sakamakon wani hadarin
ko annoba, kuma kana bukatar fahimtar
halin da yake?
•
Ka na bukartar ka fahimtar yarda
mutanen da suka shiga irin wannan hali ke
ji.
Ta kuma nuna irin halin da za su iya shiga
a gaba, da hanyoyin da mutum zai bi ya
dawo hayyacinsa har ma ya iya fahimtar
kuma ya yadda da abunda ya faru da shi
1
Rudewa wahala ko gushewar hankali na
faruwa ne yayin da mutum ya ga ko ya
kasance a wani hadari ko tashin hankali
na ganganci wanda zai iya haifar da
mummunar illa ga mutane ko ma ya yi
sanadiyyar rayuka. Ganin irin wannan,
kan sa mutum ya tsorata ko ya shiga
dimuwa da alhini. A wannan matakin sai
mutum ya rasa abin da zai yi.
ME YAKE FARUWA GA
MUTUMIN DA YA GA
MUMMUNAN HADARI KO
ANNOBA?
MISALAN HADURRA KO
ANNOBA DA KAN HAIFAR
DA BIRKICEWAR AL
AMURRA KO GUSHEWAR
HANKALI?
•
Kazamin hadurra.
•
A sanar da marasa lafiya cewa,
cutarsa na da wuyar magani ko tana
kisa farat ta daya.
•
Rashi saboda rasuwa.
•
Tashe-tashen hankula irin na, saresare da yanke-yanke ko na 'yan
daba, fyade, ko cin zarafin mata da
kananan yara, ko fashi da makami
da makamantan su.
•
Yaki ko wane iri.
•
Annoba ko sakacin Al'umma.
•
Tarzomar 'yan ta'adda.
•
Garkuwa da mutun don wata
bukata.
Firsinonin dake kurkuku ko bayi
bayan yaki.
Abu na farko da kan sami mutumin da ya
ga mummunan hadari ko annoba, shine,
mutum zai zama ya kasa gane komai, ba
zai san abinda ya ke ciki sabo da dimuwa,
har ma ya dinga ganin kamar abin be faru
ba.
Dimuwa: Yayin da dimuwa ta faru,
mutum zai fara jin:
•
Mamaki, hajijiya da batan basira.
•
Mutum sai ya zama baya son shiga
cikin jama’a ko yin abubuwan
rayuwar daya saba yi a da.
Rashin yarda:
Mutum yana rasa
yarda da abinda ya faru, domin haka sai
mutum ya sa aransa cewar wannan abu
bai faru ba. Sauran jama'a zasu yi tunanin
cewar mutumin mai kwarin zuciya ne ko
kuma mutum bai damu ba ne
Bayan wani dan lokaci, sai wadannan
tunanin su wuce, sai wasu kuma su shigo
marassa kyau.
ME ZAI FARU A GABA?
Kowa da irin yarda ya ke ji, yayin da ya ga
mummunan hadari ko annoba, da tsawon
lokacin da zai dauka kafin ya yanke
hukunci a kan hadarin da ya gani.
Yawanci mutanne suna mamaki da irin
jurewa zuciyar su. Amma dai ta kowanne
hali, mutum zai kasance wa a sahun masu:
•
Fargabar: hadarin ko annobar da ya
gani, na iya sake faruwa. Wannan fargabar
na iya sa zuciyar mutum ta yi rauni, ya
kasa jurewa, har ya shiga wani hali na
ha'ula'i.
2
duk abin daya faru ya wuce,
hankali ya kwanta abin tsoro ya
gushe.
•
Fata na gari: bayan an sami
lafiyar ciwuka da duk wa ta cuta da
idanu kan gani, hankali ya
kwanta, mutum zai fara tunanin
samun ci gaba ta rayuwa.
WADANNE ABUBUWA
MUTUM ZAI FUSKANTA?
Akwai wasu ‘yan matsaloli da mutum zai iya
fiskanta bayan halin da ya shiga. Wadannan
abubuwan sun hada da:
•
•
•
•
•
•
•
•
•
•
•
•
Rashin iya yin komai: halin iya yin
komai a kan abinda ya faru wanda
mutum yake saddakarwa don ba
abinda zai iya yi.
Rashin wadataccen bacci
Jin gajiya
Mafarke iri-iri marassa kyau
Rashin nutsuwa
Mantuwa
Tunani zai yi rauni
Ciwon kai
Karancin ko karin cin abinci
Rauni wurin mu'amullar, musamman
bangaren saduwa
Ciwukan jiki iri-iri
Saurin bugawar zuciyar
YA ZAN YI?
•
Haushi: haushi a kan abin da ya
faru da kuma da duk wanda ya yi
sanadin afkuwar hadarin.
SAI KA BAIWA KANKA LOKACI:
A zahiri, wanda duk yake a wannan hali,
ya kan dauki makwanni ko ma watanni kafin ya
dawo hankalinsa har ya yarda cewar abin da ya
faru da shi gaske ne.
•
Mai laifi: za ka ji kai kanka, ka
zama mai laifi a kan afkuwar
hadarin. Ka dinga jin kunyar cewar
ya ya kai ka tsira, amma ga wasu
sun raunana, wasu ma sun mutu.
KA YARDA ZA KA GANO ME YA FARU:
Zai fi sauki,mutum ya saddakar cewa abinda ya
faru ya riga ya faru babu abinda zai canja shi.
•
Rashin jin dadi: halin rashin jin
dadi, ba kamar in akwai
dan'uwanka ko wanda kuka shaku
a cikin wadanda suka mutu ko suka
sami rauni.
KA KUSANCI MUTANEN DA SUKA TABA
HADARI KUMA SUKA TSIRA:
In har ka taba zuwa jana'iza ko dubiyar wasu da
hadari ya ritsa da su, haka zai saukaka ma ka
wajen warware matsalarka. Saboda haka zai yi
kyau ka dinga hira da wadanda suka taba samun
matsala irin ta ka.
•
Kunya: za ka koma jin kunyar
kanka, ka kasa daurewa,
musamman idan kana son wasu su
tai make ka.
Samun sa'ida ko sauki: bayan
NEMAN TAIMAKO:
Zai yi kyau ka dinga tattaunawa da mutane a kan
a bin da ya faru. Zai kuma yi kyau, ka tambayi
'yan'uwa da abokan arziki lokaci har ka warware
ko da kuwa za su kasance cikin halin rashin
amsar da za su bayar daga farko.
•
3
MUTUM YA SAMU LOKACIN KAN
SA:
Zai yi kyau, ka ware wasu lokuta da za ka
kasance kai kadai ko da iyali ko wanda
ranka ya kwanta da.
TATTAUNAWA A KAN ABIN DA YA
FARU:
A hankali ka dinga tunawa da tattaunawa
da mutane a kan abin da ya faru.. Ka da ka
damu ko haka zai sa ka kuka. Yin hakan zai
rage maka radadin da kake fama da shi.
ZAMAN YAU DA KULLUM:
Hakika wanda yake cikin wanna hali, zai
dinga fama da rashin dandano, ya din ga jin
baya bukatar cin abinci bisa ka’ida.
Ma’ana, ya tabbatar da ya ci abinci sau uku
a rana, kamar yadda yake a tsarin cin
abinci. Ba wai sai ya take cikinsa ba, ya ci
ko ya ya yake. Ya kuma dinga motsa
jikinsa da kadan-kadan har ya saba.
SHIGA CIKIN JAMA’A:
A wasu lokuta mutum kan yi sha'awar
shiga jama'a amma bada niyar tattauna
abinda ke damunsa ba. Hakan ba laifi ba
ne, wata hanyar ce ta samun sauki.
koma kamar yadda ya saba.
KA KIYAYI SHAN GIYA KO
KWAYOYI MASU SAKA MAYE:
Ya zama dole mutum ya guji shaye-shayen
kwayoyi da giya wai don mutum ya manta
da abubuwan da ke damunsa. Shan su na
iya zama illa ga lafiyarka. In ka bi abin a
sannu, komai zai wuce.
KIYAYI GARAJEN YANKE HUKUNCI
GA MANYAN AL'AMURRANKA:
Kiyayi garajen yanke hukunci ga duk
wani babban al'amari da kake son yi.
Zabinka a wannan hali, ba lallai ne ya
zama ingantacce ba. Nemi shawarar
wadanda ka yarda dasu, don kaucewa
halin, 'da na sani’.
YAUSHE YA KAMATA KA
NEMI SHAWARAR
KWARARRU?
KIYAYEWA
Bayan alhini, mutum ya rinka kula saboda
tsautsayi na haddura da sauransu a cikin
gida ko a kan titi. Hadari ba shi da
tsayayyen lokaci.
•
ME DA ME ZAN KIYAYE?
•
RIKON ABU A ZUCIYA:
Barin abu a zuciya hadari ne, musamman
ga wanda ya tsallake siradi irin wannan.
Karo da abubuwan marassa dadi, abu ne da
ya shafi kowa, saboda haka ba abin kunya
ba ne, ka bayyana abin da ke damunka don
neman mafita. Kunshe su a zuciya na iya yi
ma illa a lafiyarka. Fito da abin da yake
damun ka fili, ko da kuwa za ka yi kuka.
KADA MUTUM YA DAUKI KOMAI
DA ZAFI:
Ba shakka kazar-kazar na iya sa mutum ya
manta da abin da ya faru da shi, to, amma
kuma hadari ne mutum ya dauki komai da
zafi, saisa-saisa, a sannu sai mutum ya
•
•
•
•
•
•
•
•
Baka da wanda za ka yi shawara
dashi.
Abubuwa sun cakude ma ka, kuma
ka kasa warware su, jin bakin ciki
haka siddan, jin kasala akai-akai ko
damuwa ba tare da wani cikakken
dalili ba.
Ka dinga jin kamar ba ka dawo
yadda kake ba, bayan mako shida.
Rashin samun wadataccen bacci
gami da mafarkai masu ban tsoro.
Ka fara tsanar mutanen da ke kusa da
kai.
Kana nisantar mutane.
Ka fara sakaci da aikinka.
Idan ka ji makusantanka na ba ka
shawarar ka nemi taimakon Likita
Ka na samun hatsari
In ka ga shan sigarinka ko barasa ya
karu, ko ka tsiri dayan biyun, ko
shan kwaya don ka manta da abinda
4
MENENE ABIN DA ZAI FARU
LOKACIN ALHINI?
MENENE MATSALA GABANIN
ALHINI:
Yayin da mutane su ka shiga halin ]imuwa
ko birkicewar kwakwalwa, sakammakon
wani hadari ko afkuwar annoba wasu
mutane suna zarcewa su samu wannan
matsalar da ake kira (1) Post-Traumatic
Stress Disorder (PTSD). Alamun da kan
nuna mutum ya shiga wannan matsalar,
sun hada da:
•
Kara shiga cikin wani yanayi na
matsanancin tunani ko mafarkai
game da hadarin da mutum ya hadu
da shi.
•
Kaucewa abubuwa da ke iya sa
mutum ya tuno hadarin da ya faru da
shi a baya.
•
Mutuwan zuciya, mutum ya dinga
ganin ya fita daga sahun masu
hankali ko lafiyayyu.
•
A ko yaushe mutum ya na tunanin
wata masifa zata same shi.
In har ka fahimci kana fuskantar matsalar
(PTSD), ka sauri ka ziyarci Likita.
WANE IRIN TAIMAKON
LIKITAN YA KE DA SHI?
Likita zai iya ba ka shawara ka je ka ga
kwararre a bangaren warkar da masu
matsalar rudewa. Irin wadannan Likitocin
na warkar da mutane ta hanyar hira da
shawara, da haka suke gane matsalar
mutum kuma su yi masa maganinta. Irin
wadannan Likitocin na samun agaji daga
iri-irin mutanen da suka sami matsala
makamanciyar ta ka, amma sun warke.
Kai kanka za ka saki jikinka, jin cewar ga
wani da ya taba samun irin matsalar da
kake fama da ita, kuma ya warke ras.
5
KO LIKITANA ZAI IYA
RUBUTA MIN
MAGUNGUNAN DA ZAN
SHA DON SAMUN LAFIYA?
Wasu lokutan shan magunguna na
taimakawa wajen samun sauki, amma
kuma yana da muhimmanci ka dinga
ziyartar Likitanka, akai-akai don tabbatar
da ci gaban lafiya.
MAGUNGUNA:
Magungunan da kan bai wa masu irin
wannan matsala su ake kira, tranqullizers.
Suna taimakawa matuka ga wajen
saukaka damuwa su kuma sa mutum ya
sami wadataccen bacci. Su kuma suna da
tasu matsalar. Idan aka wuce mako uku
zuwa hudu ana shan su, abubuwa kamar
haka na iya faruwa:
•
Za su iya daina aiki in jikin mutum
ya saba da su.
•
Zai sa ka sha fiye da kima, ma'ana,
maimakon sau daya, sai ka sha sau
biyu kafin ya yi ma magani.
•
Za su iya zamar ma jiki, ka dinga jin
in har ba ka sha ba za ka ji kamar ba
ka da lafiya.
MAGUNGUNAN RAGE
BACIN RAI
(ANTIDEPRESSANTS)
Mutum kan kasance cikin rashin laka,
jikinsa ya yi rauni ba kwari yayin da
yake halin damuwa a hadarin da ya hadu
da shi. Wannan ya sha banban da bacin
rai kawai don ya kan shafi lafiyar mutum
kuma yana dadewa a jikin mutum. Ana
iya maganin wannan matsalar ta shan
magani ko ta hira da kwararru a kan
matsalar.
This leaflet is based on material produced by
the Royal College of Psychiatrists
(www.rcpsych.ac.uk/info). © 2014
The Royal College of Psychiatrists.
Reproduced by permission.
Matakan jurewa bayan
jirkitar hankali
For more information please contact:
info@mmfng.org
or
+234 (0)807 717 7335
You can also visit
www.mmfng.org
to view the activities of the Foundation
HEAD OFFICE:
6th Floor Foreshore Towers
2A Osborne Road, Ikoyi Lagos.
Tel: +234 (0)812 957 5052
+234 (0)807 717 7335
+234 (0)816 354 6061
Email: info@mmfng.com
ABUJA OFFICE:
Asokoro Lifestyle & Business Centre
84 Kwame Nkrumah Crescent
Asokoro, FCT - Abuja.
Tel: +234 (0)812 957 5052
+234 (0)807 717 7335
+234 (0)816 354 6061
KANO OFFICE:
15 Usman Baraya Street
off Yahaya Gusau Road,
Sharada (Rinji), Kano
Kano State.
Tel: +234 803 334 0089