har abada zuciyar biladama ta kasance mai tausayi da kuma karamci
Transcription
har abada zuciyar biladama ta kasance mai tausayi da kuma karamci
‘HAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE MAI TAUSAYI DA KUMA KARAMCI’ Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa 2 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa HAKKIN MALLAKA (m) 2014 OFISHING MATAIMAKIN SHUGABAN KASA NA MUSAMMAN KAN BINCIKE DA TATTARA MUHIMMAN BAYANAI, ABUJA Ba a yarada da juyin wannan littafin domin kasuwanci, ko bayar da aronsa ta kowace fuska ba. Duk yadda ake bukatar juya littafin ba daidai ba ne, face da yardar mawallafa ba. Haka kuma duk yadda aka so yin amfani da shi, tilas a nemi rubutacciyar yarda daga mawallafa, tare da bin dokokin dab’i. 3 “AN SAMAR DA MU NE DOMIN NUNA WA JUNA SO DA KAUNA MARA MISALTUWA; AN HAIFE MU DOMIN MU GINA AL’UMMA, AMMA BA DON MU RASA TA BA” 4 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa Jawabin Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR. a wajen bikin Kaddamar da Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa a Fadar Shugban Kasa – Abuja. Laraba 16 ga Yuli, 2014 5 “ABIN SANI SHI NE BABU AL’UMMAR DA TA FI KARFIN FADAWA CIKIN BALA’I DA FITINTINU“ Inayi muku barka da zuwa wannan taro mai muhimmanci na kaddamar da Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa. Mun taru ne a wannan wuri a yau domin fara gabatar da shirin gwamnati na taimakawa mutanenmu da ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa ta kowace hanya a kasar nan. Wannan taron ba irinsa muke addu’ar gani ba. A matsayin Nigeria na matashiyar kasa mai cike da buri, naso ace a yau ina kaddamar da kwamiti akan dabarun cigaba. Amma munsami kanmu a cikin wani yanayi na takaici saboda ayyukan ashsha mara kan gado na wasu ‘yan tsirari da suke zubarda jinin mutanen da basu ji ba basu gani ba a wannan kasa tamu. Yakamata, kuma yana da muhimmanci mu tunawa taba samun kanta a haka ba. A lokutan baya, gaskiya ne, munyi fama da rikice-rikicen kabilanci dana addini. Babu wata al’umma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta, munyi kokari mun zauna da juna dai-dai da yadda zamu iya tare da fuskantar kalu-balen dake gabanmu sannan kuma munyi aiki tukuru domin karfafa dankon haduwarmu. 6 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa Idan muka sabawa junanmu, nan da nan muke Bamu taba aikata ta’addanci ba a duk lokutan da muke rikicinmu na bambamci. Amma wannan halin rayuwar namu ya sami nakasu a ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2009, a lokacin da wani dan Nigeria mai shekaru 23 yayi kokarin kunna wani makamashi dangin nakiya daya boye a cikin suturassa da yake sanye da ita a cikin Jirgin Saman Northwest Airline mai lamba 253, dake kan hanyarsa daka Amsterdam zuwa garin Detroit na Jihar Michigan, a kasar Amurka. Koda yake burinsa bai cika ba kuma an kubutar da rayukan fasinjojin 289, amma kuma wannan shirin nasa ya tabbatar da cewa ashe dai akwai wasu tsirarin ‘yan Nigeria da suka rungumi ta’addanci a matsayin tsarinsu na rayuwa. A halin yanzu zamu daina musun cewa waita’addanci ya shigo kasarmu tare da mummunan sunadaransa. Haram, wata kungiyar mutane marasa tausayi, ta daura damarar tada zaune tsaye a kasarmu. Wannan tsari nasu yayi sanadin mayarda Mata sun zama Masu takaba kuma Yara kanana sun zamo Marayu. >> CI GABA A SHAFI NA GABA 7 “SUNA TA KASHE WADANDA BA SU JI BA, BA SU GANI BA, BA TARE DA LA’KARI DA HAKKI BA. KUMA YAWANCI MASU RAUNI NE, WADANDA KE BIN DOKA DA ODA TA KASA” Sun kashe, sun raunata kuma sun saka tsoro a cikin zukatun mutane. Sun rusa kauyuka, sun lalata dukiyar mutane kuma sun ruguza hanyoyin neman abincin mutane da yawa. Sun daura damarar yaki maras ma’ana da jami’anmu na tsaro wanda ya jawo asarar rayuka da dukiya da suka wuce misali. Gaskiyar magana itace a yanzu muna fuskantar wasu mutane da zuciyarsu ta karkata zuwa yarda da yadda aka koya musu su yarda cewa aikin Ubangiji suke. Ina mai tabbatar da cewa karya fure take bata ‘ya’ya. Makiya jama’a ne kawai zasu dinga zubar da jinin mutane babu gaira babu dalili kuma su dinga fakewa da halayen mutanenmu na zamantakewa wajen watsa ra’ayinsu da cusa musu wannan ra’ayin domin su karbi na kashe jama’a. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa mun tabbatar da anyi hukuncin da ya dace ga dukkan wanda Su kuma wadanda suke da sha’awar ganin mutane a cikin yanayin ban tausayi da radadi, kuma ana kacakaca da sassan jikin mutum, jini na kwarara ta ko wace 8 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa hanya a duk lokacin da aka kaddamar da harin ta’adda, to muna sheda muku cewa babu inda zaku buya. ‘Yan Nigeria zasu tona muku asiri. Mutane nagari sun tsaneku dukkan inda kuka je a fadin duniyar nan. Muna godiya saboda goyon bayan da muke samu daga kasashen waje da kuma hadin kai da muke samu daga makwabtanmu. Wannan yana kara mana kwarin gwiwa kuma muna da tabbacin cewa kwanakin Boko Haram a kirge suke. Lokaci kawai muke jira. Yakin da mukeyi da ta’addanci yana nan daram. Idan mutane suka karanta labarin tashin bomb a kafar yada labarai, zai zama kamar tatsuniya ce ga wadanda babu ruwansu da abinda ya faru. Wata tsohuwar karin magana tana cewa idan mutum ya hangi makarar gawa zai dauka kamar daurin itace ne. Amma mu a wajenmu iyaye maza da mata da kuma iyalan mutanen da harin ta’addancin ya shafa, labarin yasha bambam. Wadan can mutanen ‘Ya’ya ne, Kanne ne maza da mata, Iyaye ne maza da mata ko kuma ‘Yanuwane na kusa dana nesa ! ‘Yan Nigeria ne nagari masu kishi da fatan alheri da kaunar kasarsu. >> CI GABA A SHAFI NA GABA 9 “MUHIMMAN MUTANE MASU MUTUNCI A IDANUN DUNIYA, SUN YI TIR DA KU” Ina kira ga dukkan ‘Yan Nigeria da su tashi su hada kai domin taimakawa jami’anmu na tsaro akan yaki da ta’addanci. Suna aiki ba dare ba rana a cikin wani yanayi mai wahala. Wani abin takaici shine idan jami’anmu na tsaro suka hambarar da shirin kawo harin abokan gaba ‘yan ta’adda sau 1000, to nasarar da ‘yan ta’adda suka samu guda daya (1) ce zata zama kanun labarai kuma zata nuna cewa kamar jami’anmu na tsao basa kokari. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da zamu maida hankalinmu akai domin mu magance su. Muna da nauyin ‘Yan Nigeria a kanmu na ganin cewa mun sami nasara akan ta’addanci. Muna bada muhimmanci ga rayuwar ko wane dan Nigeria kuma zamu cigaba da aiki tukuru babu dare balle rana domin muga mun murkushe masu wannan tayar da kayar baya. Manyan baki mata da maza, dukkan wadanda wannan ta’addanci ya shafa suna bukatar taimako. Bazamu iya musanya rayuwar yaron da aka salwantar da ita ba. Bazamu iya musanya rayukan maza da matan da aka kashe ba. Ba zamu iya mayarda karyayyun kasusuwan sassan jama’a kamar yadda suke ba. Bazamu iya dauke jimami da radadin halin kunchi da aka saka jama’a a ciki ba. Tunanin da aka sakasu a ciki abin al’ajabi ne domin wasu har iya tsahon rayuwarsu kuma akan abinda basu 10 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa san hawa ba basu san sauka ba. Iyakar abinda zamu iyayi a wannan lokacin shine mu basu gudummawar abinda zai sanya su kishin-gida akai sannan mu mika musu hannayenmu na ‘yan-uwantaka mu nuna musu cewa muna tayasu takaici da bakin ciki. Shi wannan Kwamiti na Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa yana daya daga cikin tsare-tsaren da mukeyi na kawo karshen wannan annoba. Gwamnati ta daura damarar kawo karshen wannan rikici. Ayyukan ta’addanci sun zamo annobar data haifar da daya daga cikin kalu-balen da gwamnatocin kasashe da yawa a duniya suke fama da ita. ‘Yan ta’adda suna kawo cikas ga rayuwar jama’a ta yau da kullum. Suna saka tsoro da fargaba ga jama’a kuma suna kawo cikas ga ayyukan gwamnati. Amma basu taba yin nasara ba. Basu sami nasara ba a Gabas ta Tsakiya, a Amurka, a Sin (China), a Colombia, a Italiya, a Ingila da Kenya da sauransu. Kuma baza suyi nasara ba a Nigeria. Da taimakon dukkan ‘yan Nigeria, zamu tabbatar da basu sami nasara a Nigeria ba. Dole ne Alheri yayi nasara akan Mugunta. >> CI GABA A SHAFI NA GABA 11 “AL’UMMAR NIJERIYA NA DA HAKKI A KANMU, KUMA MUN YI ALWASHIN CIKA MUSU WANNAN HAKKIN, WATO YAKI DA TA’ADDANCI” a karkshin Dattijon da ake girmamawa kuma Gwarzon namiji, General Yakubu Danjuma, wanda zai sami taimakawar kwararren ma’aikaci Fola Adeola. Zasu sami taimakawar wasu kungiyoyin taimakon jama’a na duniya da kuma wasu muhimmman ‘yan Nigeria da aka fadi sunayensu tunda farko. Zamu tabbatar da cewa mun agazawa wadanda suka shiga uku babu gaira babu dalili sanadin ayyukan ‘yan ta’adda. Yanzu zanyi wani takaitaccen bayani akan wadannan muhimman ‘yan Nigeria da suka amince suyiwa kasarsu aiki a wannan kwamiti. Bayanin tarihin rayuwarsu ya nuna cewa sun tserewa sa’oinsu. Amincewarsu suyi aiki a wannan kwamiti ya nuna babbar sadaukarwa. Wadannan hamshakun ‘yan kishinkasa sun amince su mabukata. Sun yarda su bada gudummawar lokutan da yakamata ace sunyi amfani dashi wajen bunkasa kasuwancisu ko kula da iyalansu ko shakatawa. Sun kasarmu Nigeria. Muna Godiya kwarai. Gwamnati tana kara tabbatarda shirinta na taimakon mutanen da ayyukan ta’addanci ya shafa domin rage 12 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa musu radadin ciwon da ‘yan ta’adda suka janyo. Zamu basu kulawa ta musamman domin su kara amincewa da cewa akwai mutanen kirki na gari a Shugaba, manyan baki maza da mata, zuciyar dan Adam mai tausayice kuma mai taimako ce. Ina kira ga ‘yan wannan kwamiti dasu garzaya suje su kwankwasa Ina da tabbacin cewa zaku tara dukkan abinda ake bukata domin taimakawa wajen gyara karayar da muka samu a halin zamantakewarmu. Akwai mutanen kirki da basu amince da akidar da ‘yan ta’adda ba wadanda suka maida kashe mutane da nakasasu shine halin rayuwarsu kuma suna tunanin zasu lalata tafarkin tunaninmu na alheri, to muna tabbatar musu da cewa zamu tashi tsaye domin murkushesu. Mun kafa wannan kwamiti ne domin a sami hanyar da dukkan mutane da kungiyoyin da suke da niyyar taimakawa zasu bada taimako domin ‘yan uwanmu maza da mata domin rage radadin halin kaka-nikayi da suka sami kansu babu dalili. Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare>> CI GABA A SHAFI NA GABA 13 “DUKKANIN WADANDA SUKA FADA CIKIN WANNAN BALA’I, SUNA MATUKAR BUKATAR KULAWA” haren Ta’addanci ya shafa zai taimaka wajen shirya gangami domin hada kaya da sauran gudummawar da za’a taimakawa wadanda ta’addancin ya shafa. Ina kira gu dukkan ‘yan Nigeria na gari da kuma wadanda ma ba ‘yan Nigeria ba, da sauran jama’a da kungiyoyi dasu bada gudummawarsu ga wannan asusu. Wadannan mutane suna neman taimakonmu da tausayinmu. Yakamata mu nuna cewa muna tausayawa kuma bazamu sake wasu masu wata manufa suyi sami nasara ba. Zamuyi dukkan abinda yakamata muyi domin taimakon mutanenmu da suke cikin bukata. Amma fa wannan jan aiki ne. Gwamnati ita kadai bazata iya ba. Zanyi amfani da wannan lokaci domin na godewa dukkan ‘yan Nigeria dake gida da waje da kuma kungiyoyi na duniya saboda taimako da gudummawar da suke bamu a wannan halin da muke ciki. a lokacin da muka shiga halin kaka-nikayi, taimako da gudummawar da muka samu sun kara mana kwarin gwiwar cewa akwai alamar nasara kuma kwanan nan komai zai zamo tarihi. Nigeria hadaka ce ta makwabta, ‘yan-uwa da abokai a dunkule a waje daya. A ko wane lokaci muna bukatar juna. Nigeria gaba daya iyali daya ne. 14 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa Saboda haka, Ina kira ga dukkan ‘yan Nigeria – Dalibai, Matasa, Samari da ‘Yanmata, Maza da Mata – da suyi karatun tanatsu suyi tunanin halin da wadannan mutane suka sami kansu kuma su taimaka musu. Wannan kalubalen bana masu kudi bane kawai. Gudummawa bata yawa bata kadan kuma za’a yabawa dukkan gudummawar da aka bayar. Ina kira ga ‘yan Nigeria dasu taimaka koda ta hanayar amfani da wayar Shugaba, ayyukan wannan kwamiti sune kamar haka: a. A lalubo hanyoyin da za’a kafa isasshen asusun da zai taimakawa wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa. b. A kafa ginshikin madafun da za’ayi amfani dasu wajen kafa asusun. c. A binciko mutane, yankunan jama’a, kayyayki da kadarorin da ayyukan ta’addanci ya shafa. d. A tantance kuma a lissafa irin taimakon da yakamata a baiwa dukkan wanda abin ya shafa. e. A ajiye, a rarraba kuma a dinga gudanarda asusun >> CI GABA A SHAFI NA GABA 15 “ALKAWARIN ALLAH NE ZAI TAIMAKI GASKIYA, KUMA YA KARYA SHAIDANU” taimakon da aka samu domin wadanda abin ya shafa kamar yadda yakmata. f. A fuskanci dukkan wani kalubale da zai iya tasowa kuma ayi maganinsa kamar yadda yakamata. g. A baiwa gwamnati shawara akan dukkan wata matsala da zata iya tasowa dangane da ko akan ta’addanci ya shafa. Manyan baki maza da mata, wannan wata dama ce da muka samu da zamuyi amfani da ita wajen nunawa duniya cewa ramin karya kurarre ne. Wannan dama ce da zamu tabbatarwa da mutane cewa mu duka ‘yanuwan juna ne. An haifemu mu kaunaci juna amma ba muki juna ba. An haifemu mu gina amma ba mu rusa ba. An haifemu mu tallafawa rayuwa amma ba mu kashe ba. An haifemu mu kare amma ba muyi ta’adi ba. Na gode muku da kuka saurari wannan jawabi nawa cikin natsuwa. Allah Ubangiji Yayiwa kasarmu Nigeria albarka. Nagode muku. 16 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa “INA KIRA GA ‘YAN NIJERIYA DA SU KAWO GUDUNMAWARSU HAIKAN DON TALLAFAWA WADANNAN BAYIN ALLAH, KAI KO DA TA HANYAR WAYOYINSU NA GSM NE” 17 MEMBONIN KWAMITIN (1) Gen. Theophilous Danjuma (Rtd), GCON - Shugaba (2) Mr. Fola Adeola - Mataimakin Shugaba (3) Alh. Mohammed Indimi - Memba (4) Alh. Abdulsamad I. Rabiu - Memba (5) Alh. Sani Dauda - Memba (6) Mrs. Folorunsho Alakija - Memba (7) Mr. Cosmas Maduka - Memba (8) Mr. Jim Ovia - Memba (9) Mr. Wale Tinubu - Memba (10) Air Marshal J. Wuyep (Rtd) - Memba (11) Toyosi Akerele, Mai wakiltar Youth/Civil Society - Memba (12) Alkasim Abdulkadir, Mai Wakiltar Youth/Civil Society/) - Memba (13) Chief Uche Secondus, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Kudu) - Memba (14) Alh. Tijani Tunsah, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Arewa) - Memba (15) Alh. Balarabe Musa, Mai Wakiltar Gamayyar Jam’iyyun Adawa (CNPP) - Memba (16) Alh. Sani Sidi, Shugaban Hukumar Tallfawa ta NEMA (17) Farfesa Ben Angwe, Babban Sakataren Hukumar Kwato ‘Yancin Dan Adam ta - Memba NHRC - Memba (18) Cif (Mrs.) Nkechi Mba, Mai Wakiltar Kungiyar Mata Ta Kasa (NCWS) - Memba (19) Wakilan Majalisar Koli Ta Musulunci (NSCIA) - Memba (20) Wakilan Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) - Memba (21) Air Vice Marshal Tony Omenyi, Mai Wakiltar Hukumar Tsaro Ta Kasa - Memba (22) CP Salisu Fagge, Mai Wakiltar Rundunar ‘Yan Sanda - Memba (23) Mr. Sayana Yusuf, Mai Wakiltar Jami’in Binciken Cikin Gida (SSS) - Memba (24) Wakilan Majalisar Dinkin Duniya - Memba (25) Wakilan Hukumar DFID - Memba (26) Wakilan Hukumar USAID - Memba (27) Wakilan Hukumar Red Cross ta Duniya - Memba (28) Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) - Sakataren Kwamiti 18 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa MEMBONIN KWAMITIN 19